✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 2 da 1

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a wanna wasa. Sai kuma mako mai zuwa. Da fatan kun ji dadin labaran da muka…

Abin da za mu iya kawo muku ke nan a wanna wasa. Sai kuma mako mai zuwa. Da fatan kun ji dadin labaran da muka kawo muku.

An tashi. Real Madrid ta doke Bayern Munich da ci 2 da 1 a gidan Bayern. Marcelo da Asensio ne suka zura kwallayen Madrid, yayin da Kimmich kuma ya ci na Bayern. Bayern suka fara wasan da zafi, amma da suka yi wasa da damammakin da suka samu, sai Madrid suka yi musu kifa daya kwala.

Yanzu dai mako mai zuwa ranar Talata za a sake doka zagaye na biyu a filin wasa na Bernabue na kasar Spain.

Anya Bayern za su iya tabuka wani abu a gidan  Madrid ko kuma za a sake maimaitawa ne? sai mako mai zuwa za mu gani.

94: An tashi. Bayern Munich 1 Real Madrid 2.

92: Yau Ronaldo har da yi duka.

90: An kara minti hudu.

87: Bayern sun samu dama mai kyau, amma a wannan karon, Navas ya yi kokari.

83: Kovacic ya canji Casemiro.

76: Benzemaaaaa….. Kash! Benzema ya yi idu hudu da golan Bayern, amma ya buga wa golan a jiki. Anya kuwa Benzema?

Martinez ya fita inda Tolisso ya canje shi. Da alamu ya gaji sosai.

71: Goalllllll… Ronaldoooooooooooooooo… Ayyyaaaaa.. Rafare ya hura. Ya taba kwallon da hannu kafin ya zura ta ta raga. Har yanzu Madrid 2 Bayern 1.

67: Benzama ya canji Carvajal. Carvajal ya ji rauni. Yanzu Casemiro zai koma gefen biyu. Zai sha fama da Ribery wanda shi ne le lokaci yau a ‘yan wasan Bayern.

57: Goalllllllllllllllllllllllllllllllllll… Asensio.. Asensio ya zura na biyu. Madrid 2 Bayern 1. A gidan Bayern ne kuwa?

51: Saura kiris. Riberry ya kacaccala ‘yan bayan Madrid, sannan ya jefo kwallon, amma Ramos na kusa. Rashin sa’a?

46: An dawo filin daga. Asensio ya canji Isco

An tafi hutun rabin lokaci. Real Madrid 1 Bayern 1. Kimmich ya ci zura kwallon Bayern, sai kuma Marcelo ya zura na Madrid. Sai an dawo za mu ga yadda za ta kaya.

46: Bugun tazara a kusa da gidan Madrid. Golan Madrid ya buge kwallon da kyar.

45: An kara minti 2.

44: Goaallllllllllllllllllllllllllllllllllllllllll….. Marceloooooooo…… Kaf!  Marcelo ya farke. Real Madrid 1 Bayern 1.

Hummenls. Kash! ba sa’a. Ta yi sama da yawa.

40: Kwallon bai kai na jiya zafi ba gaskiya. Har yanzu Bayern na ci 1 da nema

Kuskure daga ‘yan bayan Bayern. Amma Modric bai dauki kwallon ba. Saura kiris Madrid su farke.

35: Bayern 1 Madrid 0.

Ribery.. Kashe! Ya aka yi bai ci wannan kwallon ba?

34: Boateng ma ya ji rauni. Sule ya canje shi.

28: Goalllllllllllllllllllllllllllllll……. Kimmich ya zura wa Madrid. Tsohon dan wasan Madrid James ne ya taimaka

24: Har yanzu dai canjarasa. Babu ci a gidan Bayern.

Madriddddddddddddddddddd…. Golan Bayern ya dunkule kwallon.

Madrid suna dannen kwallon sosai, yanzu haka dai sun fi Bayern taka ledar.

16: Isco ya kai hari mai kyau, amma kwallon ta buga wani ta dawo.

Har yanzu dai wasan bai yi zafi ba. An ta tirka tirka ne a tsakiyan fili.

12: Duka sun mike, kuma an ci gaba da taka leda.

An yi karron batta da Lewandoski da Ramos. Dukansu suna jin radadi da zafi yanzu haka.

9:Alcantara ya canji Robben. Wasu masoya Bayern ba su ji dadi ba, amma da yake rauni ba yadda za a yi.

7: Robben ya fadi. Da alamu ya ji rauni domin Alcantara ya fara atisaye.

1: An fara

‘Yan wasa sun fara shigowa filin wasa.

Jama’a barkanmu da sake saduwa a wannan yammaci, inda muke kawo muku labarin wasa kai tsaye. A yau za mu kawo muku yadda za a fafata ne tsakanin Bayern Munich da Real Madrid a filin wasa Allianz Arena na kasar Jamus.

‘Yan wasa: Bayern Munich:  Ulreich; Kimmich, Hummels, Boateng, Rafinha; Martinez; Robben, Muller, James, Ribery; Lewandowski

Benchi: Starke, Wagner, Sule, Thiago, Bernat, Rudy, Tolisso 

Real Madrid:  Navas; Carvajal, Ramos, Varane, Marcelo; Kroos, Casemiro, Modric; Isco, Ronaldo, Lucas Vazquez

Benchi: Casilla, Vallejo, Benzema, Bale, Hernandez, Asensio, Kovacic

Ku biyo don samun labarin yadda wasan zai kaya.