✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Real Madrid ta barar da damar matse wa Barcelona lamba a La Liga

Asensio ya barar da bugun fenareti.

Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Mallorca a La Liga ranar Lahadi, inda Marco Asensio ya barar da fenariti.

Tun a minti na 13 da fara wasa Real ta ci gida ta hannun mai tsaron bayanta Nacho Fernandez a Estadi Mallorca Son Moix.

A minti na 59 aka bai wa Real bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da gola, Predrag Rajkovic ya yi wa Vinicius Junior keta.

To sai dai kuma Rajkovic ya tare kwallon da Asensio ya buga masa ta bangaren hagu.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki biyar tsakani da Barcelona, wadda za ta karbi bakuncin Sevilla ranar Lahadi.

Wannan ce nasarar farko da Mallorca ta samu a kan Real Madrid tun 2019 kuma ta farko a wasa 14 da suka fafata a baya.

Mallorca, wadda ta doke Atletico Madrid 1-0 a kakar nan tana ta 10 a teburi da tazarar maki tara tsakaninta da ’yan ukun karshen teburi.

Aminiya ta ruwaito yadda a ranar Alhamis Real Madrid ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Barcelona, bayan da ta ci Valencia 2-0 a gasar La Ligar a Santiago Bernabeu.