Kotu ta ɗaure magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Valencia guda uku wata takwas, bayan samum su da nuna wariyar launin fata ga ɗan wasan Real Madrid, Vinicius Junior.
Wannan shi ne karon farko a Sifaniya da aka ɗaure magoya baya, sakamakon cin zarafin ɗan wasa, bayan da mahukuntan La Liga suka shigar da ƙara a gaban kotu.
Vinicius, ya fuskanci cin zarafi daga magoya bayan Valencia a ranar 21 ga watan Mayun 2023, a gasar La Liga a filin Mestalla.
Tuni dai aka samu magoya bayan Valencia uku da laifin cin zarafin ɗan wasan na Real Madrid.
Tun farko wata 12 aka yanke hukuncin ɗaure su daga baya aka rage wa’adin, bayan da aka ƙulla yarjejeniya da mai shigar da ƙara a Sifaniya.
An kuma dakatar da magoya bayan daga shiga filin wasa na shekara uku daga kallon gasar LaLiga ko karawar tawagar Sifaniya, amma an rage hukuncin ya koma shekara biyu.
Tuni Vinicius ya wallafa a shafinsa na Instagram cewar wannan hukunci da aka yi wa magoya bayan a Sifaniya ba nasa shi kaɗai ba ne har da sauran baƙaƙen fata da suka fuskanci cin zarafin wariyar launin fata.
Shi ma a nawa ɓangaren shugaban LaLiga, Javier Tebas, ya ce wannan hukunci zai zama izina ga masu irin wannan hali na cin zarafi.