Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na dab da daukar David Alaba daga kungiyar Bayern Munich.
David Alaba na da damar tattaunawa da wasu kungiyoyin a yanzu, kasancewar kwantaraginsa da Bayern Munich zai kare a ranar 30 ga Yuni 2021.
- Diego Costa zai bar kungiyar Atletico Madrid
- Juventus na shirin gwanjon Pjanic, Costa da Higuain
- Zakarun Turai: Yadda Bayern Munich ta yi wa PSG 1-0
- Bayern Munich ta jefa Arsenal a tsaka mai wuya
Bayern Munich ta gaza cin ma yarjejeniya da dan wasan ne kan karin albashin da ya bukata na €200,000.
Sai dai rahotanni daga kasar Andalus na nuna cewa Real Madrid ta nuna sha’awarta ta daukar dan wasan bayan.
In har Real Madrid ta daidaita da dan wasan, za ta dauke shi ba tare da biyan ko sisi ba.
Jaridar MARCA, ta rawaito cewar Real Madrid ta amince za ta rika biyan Alaba miliyan €10 duk shekara.
Tun kafin wannan lokaci, Madrid ta jima tana zawarcin Alaba, ganin yadda shekaru suka cimma Kaftin din kungiyar, Sergio Ramos.
Alaba, mai shekara 28, ya buga wa Bayern Munich wasanni 404, ya kuma zura kwallo 39.