Rayuwar ’yan mata da dama da suke yi aikin da aka fi sani da ‘aikatau’ a gidajen masu kumbar susa rayuwa ce da take cike da kaskanci da tozartwa da cin zarafi daga iyayen gidansu.
Wani cin zarafin yana tasowa ne daga iyayen gidansu mata ko mazan iyayen gidan koma ’ya’yansu.
Ire-ren cin zarafin da irin wadannan ’yan aiki ke fuskanta sun hada da yin aikin ya fi karfinsu da hana su damar yin ibada a kan lokaci da hana su cin abinci a kan lokaci.
Sannan akwai korafe-korafe kan yadda ake cin zarafinsu ta hanyar fyade daga mazan gida da ’ya’yan gidan da suke yi wa aikatau.
A gefe guda kuma ba dukkan ’yan aikin ke cin moriyar kudin da ake biyan su a matsayin ladan aikinsu ba lura da cewa a wasu lokuta akan yi raba-daidai da matan da ke dauko su tare da rarraba su a gidajen mawadata don yin aikatau din.
Hallaka masu aikatau
Musgunawar da ake yi wa masu aikatau din ba ta tsaya a nan ba, a wasu lokuta ma takan kai ga kisa, kamar yadda a makon jiya aka zargi wata uwar daki da hallaka mai yi mata aikatau din a Kano.
Bayanai sun ce mai aikatau din ta rasu ne sakamakon duka da zuba mata yaji a al’auranta.
Marigayiyar mai suna Khadija Rabi’u da ke aikin wanke-wanke da share-share ta rasu ne a hannun iyayen gidanta inda ake alakanta rasuwar tata ga cin zarafin da uwar dakinta ta yi mata ta hanyar lakada mata dukan kawo wuka.
Sai dai uwar dakin marigayiyar ta shaida wa ’yan sanda cewa marigayiyar ta rasu ne sakamakon cizon muzuru.
Amma abokiyar aikin marigayiyar ta bayyana cewa ta rasu ne sakamakon dukan kawo wuka da uwar dakin nasu ta lakada mata.
Abokiyar aikatau dinta mai suna Rafi’a M. Nuhu ta ce marigayiya Khadija wadda ’yar asalin Jihar Kwara ce ta rasu ne dalilin duka da uwar dakinsu ta yi mata, inda ta ce ita ma an nemi ta sa hannu wajen dukan marigayiyar.
“Bayan mun dawo daga unguwa da daddare sai muka tarar Khadija ba ta yi aikin da aka sanya ta ba, inda ta ce ba ta jin dadi.
“Hakan ya sa uwar dakinmu ta shiga dura mata ashariya kafin ta dauko tabarya ta rika dukan ta da ita.
“Sannan ta umarce ni in je in dauko muciya ni ma in dake ta. Har na fara dukanta sai tausayin ta ya kama ni, ganin tana kuka sai na kyale ta.
“A nan sai uwar dakinmu ta dauko wani karfe ta caka mata a al’auranta sannan ta dauko ya ji ta barbada mata a gabanta,” inji ta.
Sai dai wadda ake zargin, Fatima Hamza wadda aka fi sani da Ummi ta ce ’yar aikinta ta rasu ne sakamakon cizon muzuru ba kamar yadda ake yadawa ba.
“Dama kwana biyu Khadija ba ta da lafiya sakamakon cizon da muzuru ya yi mata.
“Ashe dama ya dade yana cizonta ban sani ba sai a wata rana ta fito daga daki da gudu har ta buge fuskarta.
“Lokacin da nake bincikar ta ce ta gaya min cewa ai ya cije ta a dan yatsa.
“Daga nan na sa aka kai ta asibti aka ba ta magani,” inji ta.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano dai ta yi watsi da bayanin uwar dakin marigayiyar na musanta zargin cin zarafin da ta yi ga marigayyiyar inda ta gurfanar da ita a gaban kotu bisa tuhumar ta da laifin kisan kai.
Kuma tuni Alkalin Kotun Majistare ta 8 da ke Gyadi-Gyadi Mai shari’a Ibrahim Khaleel Mahmood ya bayar da umarnin tsare wadda ake zargin a kurukuku tare da dage shari’ar zuwa ranar Talata mai zuwa 16 ga Fabrairu don ci gaba da sauraron shari’ar.
Wata ta rataye kanta
A karshen watan jiya ma wata budurwa mai suna Bahijja wadda ta fito daga Gombe mai kimanin shekara 16, aka iske gawarta a rataye a daki a gidan da take yin aikatau.
Ana zargin budurwar ta rataye kanta ne a ranar Asabar din makon shekaranjiya bisa dalilin da ba a gano ba.
Rahotanni sun ce Bahijja tana aikatau ne a wani gida da ke Titin Zoo a birnin Kano kuma a nan ne aka iske ta rataye.
An dai tsinci gawar marigayiya Bahijja ce a daki inda ake zargin ta rataye kanta da misalin karfe 10 na dare.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka kai gawar Bahijja zuwa Asibitin Murtala.
DSP Kiyawa ya kara da cewa za a zurfafa bincike don gano dalilin da ya sa ta kashe kanta.
Sai dai duk kokarin Aminiya ta yi don jin ta bakin iyayen daakinta a gidan da marigayiya Bahijja ke aiki, ya ci tura inda suka ki yarda su yi magana da manema labarai.
Duk da har zuwa yanzu ba a gano dalilin da ya sa ta dauki wannan mataki ba, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suna zargin cewa mutuwar tata ba za ta rasa nasaba da wani cin zarafi da aka yi mata a gidan aikin ba.
Uwargida ta tilasta ’yar aiki cin bayan gidanta
Idan za a iya tunawa Aminiya ta taba ruwaito yadda wata uwar daki ta tilasta wa ’yar aikinta cin bayan gidanta bayan da ta yi kashi a kasa.
’Yar aikin wadda ’yar asalin garin Dan Hassan ne a Karamar Hukumar Garun Malam da ke Jihar Kano ta samu bacin ciki ne, inda hakan ya sa kashin ya kubuce mata kafin ta shiga ban-daki, kuma hakan ya sa matar ta tilasta ta cinye bayan gidan.
A wancan lokaci duk da cewa hukumomin kare hakkin dan Adam sun yi kokarin shiga lamarin amma haka maganar ta bi ruwa musamman ganin cewa iyayen yarinyar ba su dauki abin da muhimmanci ba domin kwanaki kadan da faruwar lamarin yarinyar ta dawo cikin birni tare da ci gaba da aikatau a wani gida na daban.
‘Abin da ya sa muke aikatau’
Aminiya ta tattauna da wata yarinya mai suna Sabira da yanzu take aikatau a wani gida a Kano, inda ta ce suna yin wannan aiki ne don su tallafa wa kansu wajen samun kudin kayen daki.
“Mu kanmu mun san ana wulakanta mu amma saboda ba mu da wata hanya ya sa muke hakuri.
“Kin san a kauye iyayenmu ba su da karfi shi ya sa muke yin wannan aiki saboda yawancinmu muna fitowa ne don neman kudin kayan daki.
“Da kudin da ake biyan mu muke samun na sayen kayan daki,” inji ta.
Da take lissafo wahalhalun da take fuskanta ’yar aikin ta ce, “Ina yin aiki tun daga Sallar Asuba har zuwa lokacin kwanciyar barci ba tare da hutawa ba.
“Idan na tashi zan fara dora ruwan wankan yara tare da shayi da kuma abincin da za su tafi da shi makaranta, wanda yawanci dankali ne da soyayyen kwai.
“Sannan in je dakunan yaran in taso su in yi musu wanka in shirya su, in ba su shayi su sha; Sannan ne matar gidan za ta fito ta dauke su zuwa makaranta.
“Daga nan sai in koma in dora girkin karin kumallo. Sai kuma in yi shara in yi goge-goge, sannan in karya.”
“Bayan nan ne zan hada wankewanke in yi. Kafin in gama gyaran gidan sai ki ga lokacin dora abincin rana ya yi.
“Idan na gama lokacin yaran sun dawo sai in kula da su in ba su abinci in yi musu wanka in shirya su don zuwa Islamiyya.
“Bayan ta tafi kai su Islamiyya zan tsaya in sake gyara gidan da wanke kwanukan da suka bata.
“Daga nan in dora girkin dare. Haka dai zan ci gaba da ayyuka har lokacin barci,” inji ta.
‘Ba laifin iyayen kadai ba ne’
Da yake jawabi kan cin zarafin da ake yi wa yaran, wani magidanci Malam Aminu Habib Mandawari ya ce duk da cewa an fi ganin laifin iyayen yaran da ake turo su aikatau birane, to amma akwai bukatar jan hakalin mawadata da ke daukar irin wadanan yara su san cewa aiki kadai suka dauke su ba bauta ba.
“An fi dora alhaki a kan iyayen yaran amma su ma mawadatan da ke daukar wadannan aiki ya kamata su ji tsoron Allah, su sani cewa wadannan yara aiki suka dauke su ba bauta ba.
“Su tausaya musu tare da ba su hakkokinsu. Ya kamata su san cewa suna amfanuwa daga yaran lura da cewa akwai mutanen da ba su taba iya rayuwa sai da masu yi musu hidima a kusa.
“Ina gani duk wanda zai yi maka wani aikin da ya zama kai za ka yi, ya taimaka maka koda kuwa kana biyansa kudi,” inji shi.