✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar talakawan Najeriya a yau  

Talakawan da ke ajin farko yanzu sun samu koma baya zuwa ajin mabarata.

Mubarak Ibrahim Lawan ya rubuto wannan makala ce daga Jihar Kano kan rayuwar talakan Najeriya a yau.

Ya rubuto cewa, idan Naira dubu 20 ce kudin cefanenka a shekarar 2015 zuwa 2016, yanzu sai ya kai Naira dubu 80 zuwa 100.

Alaji kar ka yi musu! Tunano kudin manyan kayan abinci a wancan lokacin.

Shinkafar Thailand da kake siya kasa da dubu 10 a Kano, a yau dubu 27 ce.

Man girki, taliya, makaroni, fulawa, gero, masara, dawa da wake, babu wanda bai ninka kudinsa sau 2 ko 3 ba.

Sai ka rasa wai wane irin tsarin tattalin arziki wannan mulkin ya dora kasar a kai.

Talauci, Kinko Sarkin Karfi, neman kayar da kowa yake fa.

Masu matsakaicin karfi a da, yanzu duk sun koma kasa, sahun talakawa ajin farko.

Su kuma talakawan da ke ajin farko a da, yanzu sun samu koma baya zuwa ajin mabarata.

Don haka adadin ’yan Allah-ba-ku-mu-samu da na ’yan ta’adda ya fi kowanne hauhawa!

Ka leka gurin masu awo ka ga yadda ake rububin siyan diddigar indomie ta Naira 20 zuwa 50.

Ka ga yadda ake siyan taliya da ta zo da matsala daga kamfani a Naira 100; da yadda mutane ke kokawar siyan rogon danwake tunda fulawa ta fi karfin talaka.

Ga yadda ake siyan tattasai da tumatir da attarugu gwalagwaji; ka ga yadda ake dakawa garin kwaki wawa duk da ya yi tsadar da bai taba yi ba a tarihi!

Alaji ka kalli yadda ’yan matan kauyuka da ke siyar da gyada da rogo suke ciniki.

Hakanan ka kalli yadda masu siyar da kwado a baro ke karuwa a titina tunda ana kwantar da yunwa da shi!

Da safe kuwa, an fara hakura da kosai tunda wake ya zama dan sarki! Fanke, ’yar tsala, wainar rogo (taka yaga), awara, faten tsaki, danwake, wainar Fulawa, dankalin Hausa da dai sauransu, duka su ne karin kumallo a yanzu.

Su mai girma kwai da indomie, dankalin turawa da doya; tabdijan! Ai sai ranakun da dawa tai nama ake tunawa da su!

Tabbas talaka na shan murji da matsa tunda taliya ’yar murji ma ta fara fin karfinsa a wannan mulki!

Barayin gwamnati, ’yan bindiga da masu satar mutane, sai kuma ’yan kasuwa da ke da karfin jari kadai ke jin dadin wannan gwamnati!

Don haka Addu’armu dai ita ce, ya Allah duk wanda Ka ba shi mulkin al’ummar Annabinka Muhammad (SAW), kuma ya kuntata musu, Ya Allah ka kuntata masa a nan duniya da lahira shi ma.

Idan kuma ya kyautata ya tausaya musu, Ya Allah ka kyautata masa, Ka tausaya masa shi ma!