More Podcasts
A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya.
Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar.
Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka?
- NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma
- DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’
Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai shafi ɗan Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan: https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16955648-yadda-fa-uwar-farashin-anyen-mai-zai-shafi-rayuwar-yan-najeriya.mp3?download=true