✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar mai bin Yesu Kiristi a yau da kullum (1)

Muna cikin zamani wanda masu bin Yesu Kiristi da yawa sun bar bin umarnin Ubangiji Allah game da rayuwar yau da kullum domin kalubalen da…

Muna cikin zamani wanda masu bin Yesu Kiristi da yawa sun bar bin umarnin Ubangiji Allah game da rayuwar yau da kullum domin kalubalen da suke fuskanta. Abu guda wanda dole mu gane shi ne, Allah ba Ya sakewa ko kadan; duk abin da Yake so masu bi su yi a da, shi ne abin da Yake so mu ci gaba da yi yau, bai canja ba, kuma ba zai canja ba har abada. Komai tunaninmu game da abin da yake faruwa da masu bi a yau; ba zai taba canja nufin Allah ba, ba za mu iya juya maganar Allah Ya fadi wani abu daban da abin da an rigaya an rubuta a cikin Littafi Mai tsarki ba. Zan yi kokari in dauki fanni daya a wannan sashi da ya kunshi rayuwarmu ta yau da kullum.
Maganar Allah na cewa, “Amma ku masu ji, ina ce muku, ku yi kaunar magabtanku, ku yi wa makiyanku nagarta, ku albarkaci masu zaginku; wadanda suke wulakanta ku, ku yi musu addu’a. Wanda ya mare ka a wannan kumatu, ka juya masa wannan kuma; wanda ya amshe maka mayafi kada ka hana masa riga kuma. Ka bayar ga kowane mai rokonka; wanda ya kwace maka dukiyarka kuma, kada ka bide su a gare shi. Kuma kamar yadda kuke so mutane su yi muku, ku yi musu haka nan kuma. Idan kuwa kuna kaunar masu kaunarku, wane abin godiya ke gare ku? Gama har da masu zunubi suna kaunar masu kaunansu. Idan kuma kuna yin nagarta ga wadanda suke yi muku nagarta, wane abin godiya ke gare ku? Gama har da masu zunubi suna yin wannan. Idan kuwa kuna ba da rance ga wadanda kuke sa zuciya za ku samu a gare su, wane abin godiya ke gare ku? Har da masu zunubi suna ba da rance ga masu zunubi, domin su samu kuma misalin abin da suka bayar. Amma ku yi kaunar magabtanku, ku yi musu nagarta, ku ba da rance, kada ku fidda zuciya dadai; ladarku kuwa mai girma ce, za ku zama ’ya’yan Madaukaki, gama Shi mai alheri ne ga marasa godiya da miyagun. Ku zama masu jinkai, kamar yadda Ubanku Mai jinkai ne. Kada ku zartar, ku kuma ba za a zartar muku ba: Kada ku kayar, ku kuwa ba za a kashe ku ba: ku kwance, za a kwance ku kuma: ku bayar, za a ba ku, mudu mai kyau, dankararre, girgizajje, mai zuba, za su bayar cikin kirjinku. Gama da mudun da kuke aunawa da shi za a auna muku.” (Luka:6: 27–38).
Bisa ga yardar Ubangiji Allah; za mu dauki lokaci muna yin bincike kan wurin da muka yi karatu. Binciken da za mu yi, zai kunshi ababe kamar haka:
Ku yi kaunar magabtanku
Ku yi wa makiyanku nagarta
Ku albarkaci masu zaginku
Ku yi addu’a domin wadanda suke wulakanta ku
Kada ku rama mugunta da mugunta
Ku bayar hannu sake
Ku yi wa mutane kamar yadda kuke so mutane su yi muku.
Ina so mu sani cewa, bin Yesu Kiristi dole ne ya zama daga cikin zuciyarmu. Yana da kyau mu yi wa Allah sujada; mu kuma bauta maSa, amma abin lura a kullum shi ne; duk ibadarmu idan ba mu da zuciyar aikata abin da muka lissafa a bisa ba; duk ibadar banza ce. Adalci na gaskiya ya kunshi tafiya cikin kauna; kamar yadda muke; kowane mai bin Yesu Kiristi dole ne ya sani cewa kodayake muna cikin wannan duniya, amma mu ba na duniya ba ne; maganar Allah na cewa: “Wadannan abubuwa nake umartarku, domin ku yi kaunar juna. Idan duniya ta ki ku, kun sani ta rigaya ta ki ni tun ba ta ki ku ba. Da na duniya ne ku; da duniya ta yi kaunar nata; amma domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zabe ku daga cikin duniya, saboda wannan duniya tana kin ku. Ku tuna da magana wanda na fada muku. Bawa bai fi Ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mani tsanani, za su yi muku tsanani kuma; idan suka kiyaye maganata, su kiyaye taku kuma. Amma wannan abu duka za su yi muku saboda sunana, domin ba su san shi Wanda Ya aiko ni ba.” (Yohanna:15:17–21).
Muna cikin mawuyacin zamani ne sosai, masu mugunta suna ko’ina kewaye da mu; suna kuma neman dalilin da za su aikata abin da suka saba yi wato mugunta, shi ya sa masu bi da dama suna tunani game da irin rayuwarsu a yau; suna tsammanin idan suka yi tafiya bisa ga umurnin Allah; za su cutu; amma komai wahala, komai tsanani; ba za mu taba janyewa daga koyarwar ubangijinmu Yesu Kiristi ba, domin hanya guda wadda za a iya bambanta tsakanin masu bin Yesu Kiristi da sauran mutanen da ke duniya – ita ce cewa; ta wurin ikon Ruhu Mai ttsarki, za mu iya yin abubuwa da yawa da mutum ba zai taba iya yi ta wurin karfin kansa ba – NUNA kAUNA GA MAkIYI. Maganar Allah na koya mana da cewa “Ku ne gishirin duniya: amma kadan gishiri ya rabu da dandanonsa, da mai za ya gyaru? Nan gaba ba ya da amfani ga komai ba, sai dai a yar, a tattake karkashin sawun mutane. Ku ne hasken duniya. Birnin da ke kafe bisa tudu ba ya boyuwa. Kuma ba a kan kunna fitila, a sa ta karkashin akwashi ba, amma bisa teburi; sai ta haskaka wa dukan wadanda ke cikin gida. Haka ku ma ku bari haskenku ya haskaka gaban mutane, domin su ga ayyyukanku masu kyau, su girmama Ubanku Wanda ke cikin sama.” (Matta:5:13–16).  Duk mai bin Yesu Kiristi da yake son ya yi zaman haske a wannan duniya dole ne ya shirya domin masu gaba da za su taso su kalubalance shi. Zaman haske shi ne; yin ayyukan kawar da duhu, duhun nan kuwa shi ne kawar duk abin da yake gaba da maganar Allah. Shaidan a kullum yana neman hanyar da zai sa mutum ya ki bin umarnin Allah; ya saba wannan tun daga farko. Har zuwa yau, akwai mutane da yawa da Shaidan ne ke mulki a cikin zuciyarsu; ba su da iko su ki aikata nufin Iblis, shi ya sa zai iya aikarsu ko suna so ko ba su so. Abu guda wanda nake so mu lura da shi; shi ne, idan har muna tafiya cikin haske, mutane za su ga ayyukanmu masu kyau su kuma girmama Ubangiji Allah Wanda ke cikin sama.

Za mu ci gaba da wannan bincike mako mai zuwa domin mu gane yadda ya kamata mu yi rayuwa a cikin wannan duniya tamu ta yau. Mu ci gaba da yin addu’a domin shugabaninmu; Ubangiji Ya ba su hikima domin su yi shugabanci da tsoron Allah. Ubangiji Allah Ya albarkace ku duka, amin.