✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwa ’yar faduwa da tashi ce

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran…

Kamar yadda muka saba, yau ma Allah Ya sake kawo mu wani makon, kuma za mu ci gaba da kawo maku tambihi game da sinadaran yaukaka rayuwa. Jama’a, ina yi maku sallama, Assalamu alaikum.
Abu ne da kowa ya sani cewa, rayuwarmu na cike da kalubale, wanda haka kan sanyaya gwiwar wasu, har ma su wofintar da dukkan al’amuransu, sannan su fitar da tsammanin samun nasara. Wannan bai dace ba, domin kuwa dama haka al’amuran rayuwa suka gada, idan yau an hau tudu, to gobe kuma sai a samu gangara, a gangaro zuwa ga nasara da cimma bukata. Don haka, maudu’inmu na yau zai yi tsokaci ne game da wannan al’amari, yadda za mu fahimta da cewa bai kamata mu karaya da rayuwa ba, komai tsanani, komai runtsi.
A duk inda muka samu kanmu, kuma a duk yanayin da muka shiga, abu na farko da za mu sanya a zukatanmu shi ne, za mu iya yin nasara a rayuwa. Duk kalubalen da ya tare mana gaba, mu yi ta maza, mu tunkare shi gaba-gadi, sannan mu amince da cewa lallai za mu iya yin nasara a kansa. Ba zama za mu yi ba mu shantake, za mu sanya azama ne, sannan mu maida hankali yadda ya kamata, sannan mu bi hanya mafi dacewa da za ta kai mu ga biyan bukata. Idan muka yi haka, babu shakka ga nasara nan a hannunmu.
Sai dai wani abin da ya kamata ya zama fandeshi kuma ya zama abin da za mu rika tunawa da shi, shi ne mu sanya a zuciyarmu cewa bayan wahala sai dadi. Don haka, a duk lokacin da muka fadi kasa a yayin cimma wata bukata, kada mu dauka cewa wannan ne karshen rayuwarmu, kada mu dauka shi ke nan an yi ruwa an dauke, don haka ba za mu cimma nasara ba. Kada mu yi haka, mu mike tsaye kawai, mu kakkabe jikinmu sannan mu sake tunkarar kalubalen; za mu ci nasara da yardar Allah.
Naci, Hausawa sun ce damben kuturu ne. To, lallai ita rayuwa tana bukatar naci, domin babu wani kalubale da zai kauce daga hanyarka, dole sai ka yi nacin kawar da si. Muddin kuwa aka sanya naci kan yin duk wani abu, komai wahalarsa, wata rana zai zama labari. Za a cimmasa. Misali, idan kai dalibi ne, kana koyon wani karatu, za ka fuskanci kalubale da zai kawo maka wahala a zuciya da kwakwalwa, wanda kuma zai kawo maka tarnaki ga koyon wannan karatu. Babu mamaki ma ka ji cewa ba ka kaunar darasin da ake koya maka, ko kuma ka ji cewa ba ka sha’awar malamin. Wannan duk suna daga cikin kalubalen da za su yi maka tarnaki ga cimma burinka na koyon karatun. Me ya kamata ke nan ka yi? A nan, ya zama dole ka wanke zuciyarka, ka maida ita tamkar dutse, yadda za ka tursasa ta, ta fuskanci koyarwar gaba gadi, sannan ka daure wa duk wani ciwo da rashin jin dadin da kake na koyon karatun. Bayan haka, sai ka sanya naci da maida hankali. Idan ka kasance haka, sai mafarkinka ya zama gaskiya, sai nasararka ta zama ta bayyana karara.