✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwa ’yar faduwa da tashi ce (2)

daya daga cikin kalubalen rayuwa, wadanda kuma suke kawo cikas ga mai son samun nasarar wani abu, shi ne maganganun mutane. Mafi yawan lokaci, idan…

Bayan aiki tukuru, mutum na bukatar addu’a domin samun nasarar rayuwa!daya daga cikin kalubalen rayuwa, wadanda kuma suke kawo cikas ga mai son samun nasarar wani abu, shi ne maganganun mutane. Mafi yawan lokaci, idan mutum ya tunkari yin wani abu, zai ji maganganun mutane daban-daban, wadanda idan ya biye masu, sai su dankwafar masa da niyya, kila ma daga nan ya ce zai watsar da al’amarin. Ke nan sun yi nasarar hana shi cimma wani burinsa na rayuwa ke nan. Misali, kana iya cewa, bari in fara kasuwanci. Jin haka sai abokai su fara yi maka dariya, ko su rika yi maka shegantaka, suna cewa ka fi karfin haka, da dai sauran maganganu na karya gwiwa irin wadannan. Kada ka saurare su, ci gaba da nufinka, bayan wani lokaci, za ka cimma nasara.
Ita nasara fa babu ruwanta da gado, babu ruwanta da cewa babana kaza ne, innata kaza ce, yayana kaza ne. Kowa na iya samun nasara, muddin dai ya bi matakan da suka dace. Kana gani, dan talakka sai ya zama sarki, idan dai ya bi matakan zama sarkin. Kana gani dan attajiri zai tsiyace, idan bai bi matakan zama attajirin ba. Haka kuma dan malami na iya zama kuntukurmin jahili, muddin bai bi matakan da zai samu ilimi ba. Don haka, rayuwa ’yar tashi a nema ce, kuma neman za a yi shi ne ba da sanyin jiki ba. Za a jajirce, sannan a maida hankali, idan da rabo sai nasara ta kawo jiki da kanta.
Bari mu ba da wani misali da zai yi mana ishara da abin da muka fada a sama. Shekaru aru-aru da suka gabata, an samu wani yaro da aka kai shi makaranta. Bayan lokaci sai malamansa suka kore shi, suka aika wa iyayensa takardar da ke cewa, yaron nan dakiki ne, shashasha ne, ba zai iya koyon komai ba a rayuwarsa. Mahaifiyar yaron nan ta ji ciwo sosai da karanta wannan takarda. Sai ta jajirce, ta ce, in Allah Ya yarda, sai na koya wa yarona ilimi, kuma sai ya yi nasara a rayuwa.
Haka kuma abin ya kasance, sai ga shi bayan shekaru, yaron da aka ce wa dakiki ya zama haziki, ya zama zakakuri a fannin kimiyya. Kun san ko wane ne wannan? Ba kowa ba ne sai Mista Thomas Edison, wanda shi ne ya fara kirkiro kwan lantarki. Ba wannan kadai ba ma, shi ne ya kirkiro hoto mai motsi, watau kimiyyar da ake amfani da ita wajen shirya fina-finai da shirye-shiryen talabijin. Kafin ya bar duniya kuwa, tarihi ya nuna cewa, ya kirkiro abubuwa masu tarin yawa, wadanda ke amfanar al’umma har zuwa yau din nan, kuma za su ci gaba da amfanar al’umma har zuwa karshen rayuwar al’umma.
Wannan ya nuna mana cewa ba a sanyin jiki da rayuwa. Idan wannan kofar ta rufe maka, kwankwasa wata, za ta iya budewa sannan ka shiga ka samo nasara. Irin wannan ta sha faruwa ga mutane daban-daban na fadin duniyar nan, watau ba ga Thomas Edison kadai ba. Haka ma ta taba faruwa ga shahararren mai kera fasahar na’ura mai kwakwalwa, wanda aka ce shi ya fi kowa kudi a duniya yanzu. Ina batun Bill Gates ne, wanda shi ma asalinsa korarre ne daga makaranta, amma da yake bai amince rayuwa ta karya shi ba, sai ya maida hankali da kashin kansa, har Allah Ya ba shi sa’a ya samu nasarar rayuwa. A yau kuwa ga shi sunansa ya kai ko’ina cikin duniya.
Don haka, dan uwa, ’yar uwa, za ku iya samun nasarar rayuwa. Mu mike tsaye, mu sanya azama, mu tunkari al’amuranmu da gaskiya. Mu bi dukkan matakan da suka dace, lallai kam bayan duhu, sai mun cimma haske!