Mutane sun iya yin shirye-shiryensu, amma cikawa ta Ubangiji ce. Za ka yi tsammani kowane abu da ka yi daidai ne, amma Ubangiji yana auna manufarka. Ka roki Ubangiji, ya sa albarka ga shirye-shiryenka, za ka kuwa yi nasara cikin aikata su. Kowane abu da Ubangiji ya yi yana da makoma, makomar mugun kuwa hallaka ce. Ubangiji yana kin kowane mutum da ke fariya. Irin wannan mutum ba zai kubuta daga hukunci ba. Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka. Lokacin da ka yi abin da Ubangiji ke so, ka iya mai da makiyanka su zama abokai. Gara ka sami kadan ta hanyar gaskiya, da ka tara abu mai yawa ta hanyar zamba. Kana iya yin shirye-shiryenka, amma Allah ne ke bi da kai cikin ayyukanka. Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a koyaushe yakan yanke shawarar da ke daidai.Ubangiji yana son ma’aunai su zama na gaskiya, kowane abin sayarwa kuma ya zama daidai. Sarakuna ba za su iya jurewa da mugunta ba, gama adalci ke sa hukuma ta yi ƙarfi. Sarki yana so ya ji gaskiya, zai kuwa ƙaunaci mutanen da ke fadar gaskiya. Mutum mai hikima yakan yi kokari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani. Alherin sarki kamar gizagizai ne masu kawo ruwan sama a lokacin bazara, akwai rai a ciki. Yana da kyau, ya kuma fi kyau a sami hikima da ilimi fiye da zinariya da azurfa. Mutumin kirki yana tafiya a hanyar da ta kauce wa mugunta, saboda haka ka kula da inda kake tafiya, za ta ceci ranka. Girmankai jagora ne zuwa ga hallaka, fāriya kuwa zuwa ga fāɗuwa. Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu tawali’u, da ka zama ɗaya daga cikin masu girmankai, har da za ka sami rabo daga cikin ganimarsu. Ka mai da hankali ga abin da aka koya maka, za ka yi nasara. Ka dogara ga Ubangiji, za ka yi farin ciki. Mutum mai hikima, wanda ya isa mutum, akan san shi ta wurin hazikancinsa, kamar yadda kalmominsa suke da dadi, haka ma rinjayarsa take. Hikima mabubbugar rai ce ga mai hikima, amma bata lokaci ne a yi ƙoƙarin koya wa dakikai.
Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya fada yakan yi rinjaye kwarai. Kalmomi masu dadi suna kama da zuma, suna da dadin dandana, suna kuma da amfani domin lafiyarka. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka. Marmarin cin abinci yakan sa dan kodago ya yi aiki da kwazo, domin yana so ya ci ya koshi. Mutumin da yake jin dadin yin mugunta yakan tafi yawon nemanta, mugayen maganganunsa kuna suke kamar wuta. Mugaye sukan baza jita-jita, suna zuga tashin hankali, suna raba aminai. Mutum mai ta da zaune tsaye yakan rudi abokansa, ya kai su ga bala’i.Ka kula da mutane masu murguda baki suna kada gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan. Furfurar tsufa rawanin daraja ce, sakamako ne ga ran mai adalci. Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.Mutane sukan jefa kuri’a don su san nufin Allah, amma Allah da kansa ne yake ba da amsa.
Gara a ci ƙanzo da rai a kwance, da gida cike da liyafa, amma cike da tashin hankali. Bara mai wayo yakan sami iko a kan shashashan ɗan maigidansa, har ya sami rabo a cikin gādon. Zinariya da azurfa da wuta ake gwada su, zuciyar dan adam kuwa Ubangiji ne yake gwada ta. Mugaye sukan kasa kunne ga mugayen dabaru, makaryata kuma sukan kasa kunne ga karairayi. Wanda ya yi wa matalauci ba’a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka. Tsofaffi suna fāriya da jikokinsu, kamar yadda samari suke alfarma da iyayensu maza. Mutumin da yake kamili ba ya fadar karya, haka ma wawa ba zai fadi wani abin kirki ba.
Wadansu mutane suna tsammani cin rashawa yakan yi aiki kamar sihiri, sun gaskata zai iya yin kome. Idan kana so mutane su so ka, ka rika yafe musu sa’ad da suka yi maka laifi. Mita takan raba abuta. Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa daya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an doke shi sau dari. Mutuwa za ta zo wa mugaye kamar mugun manzo wanda a koyaushe yana so ya kuta tashin hankali. Gara mutum ya gamu da beyar ta mata wadda aka kwashe mata kwiyakwiyanta, da ka gamu da wadansu wawaye suna aikin dakikancinsu. Idan ka sāka alheri da mugunta, ba za ka iya raba gidanka da mugunta ba, faufau.Mafarin jayayya kamar barkewa madatsar ruwa ne, sai a tsai da ita tun ba ta habaka ba. Da wanda ya baratar da mugun da wanda ya kā da adali, duk abin ki suke ga Ubangiji. Kashe kudi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani. A koyaushe abokai sukan nuna kaunarsu, ‘yan’uwa kuma, ai, don su dauki nawayar juna suke. Sai mutum marar tunani ne kadai zai dauki lamunin basusuwan makwabcinsa. Shi wanda yake son zunubi, yana son wahala ke nan, wanda kuma yake yin fāriya a dukan lokaci yana neman tashin hankali ke nan. Mutumin da yakan yi tunanin mugunta, ya kuma hurta ta, kada ya sa zuciya ga samun abin kirki, sai dai bala’i kadai. Mahaifi wanda dansa yake yin abubuwan wauta, ba shi da kome sai bacin rai da bakin ciki. Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya. Zama da bakin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.
Karin Magana 16,17:1-22