✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rasuwar Janar Attahiru ta girgiza ni —Na’Allah

Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya,…

Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Ibn Na’Allah ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Laftanar Janar, Ibrahim Attahiru.

Janar Attahiru ya rasu ne a hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a Kaduna, wanda shi ne na biyu da jiragen Rundunar suka yi a bana.

“Labarin hatsarin jirgin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya wanda Shugaban Rundunar Sojin Kasa yake ciki ya girgiza ni.

”Hantata ta kada bisa yadda mutumin kirki irin Laftanar janar Ibrahim Attahiru da sauran hafshoshi suka kwanta dama a kokarinsu na kare kasar nan.

“Ina mika ta’aziyyar Kwamitin Sojin Sama na Majalisar Dattawa ga daukacin ’yan Najeriya da iyalan mamatan.

“Ubangiji Allah ina rokon Ka, Ka lullube su da RahamarKa madawwamiya, Ka sa su a Aljanna Fidausi,” inji sakon ta’aziyyar da ya fitar.