✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ke hana ci gaban noma a Nijeriya — Suleiman

An gano cewa, rashin zuba jari mai ƙarfi da kuma mai da hankali wajen bunƙasa harkokin noma daga gwamnati a matsayin wasu dalilan da ke…

An gano cewa, rashin zuba jari mai ƙarfi da kuma mai da hankali wajen bunƙasa harkokin noma daga gwamnati a matsayin wasu dalilan da ke hana ruwa gudu wajen mai da Nijeriya zama ƙasar da ke iya dogara da kanta kan harkokin noma da wadata ƙasa da abinci.

Wani ƙwararre kanharkokin gona kuma tsohon Kwamishina da ke kula da ma’aikatar harkokin noma a Jihar Bauchi, Alhaji Bala Othman Suleiman ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi.

Ya ce, tun da farko lamarin noma yana tafiya yadda ya kamata, musammanawajen 1960, saboda a lokacin gwamnatoci sun yi ƙoƙarinsu wajen inganta harkokin noma, sun bai wa manoma dukkan goyon bayan da suke buƙata, kafin manomi ya yi noma, an fada masa abin da ake buƙata ya noma na ci da na sayarwa, an horas da shi kan abin da zai noma, an samar masa da kasuwar da zai sayar da kayan nomansa bayan ya girbe, kafin ya fara noma, ya san farashin da zai saida amfanin noma, ya san kudin da zai sayar da kilo, ya san kudin da zai sai da labar gyada da labar auduga da sauran kayayyaki kuma sai wanda ya ga dama zai sayar ba tilas a ciki, ya san ribar da zai samu, wanda shi yake ƙarfafa shi wajen yin noman da gaske.

Suleiman ya ce, daga baya sai aka riƙa samun kurakurai da rashin mai da hankali wajen bunƙasa harkokin gonar, kuma ba a mai da hankali ba sai dai a dan tsakuri wani abu cikin kasafin kudi, a ce an ware wa noma daga ƙarshe ma aka ce an cire tallafi ga noman, tun ba a gina shi ba.

Ya ce, kowace ƙasa tilas ne gwamnatoci su zuba jari mai ƙarfi don noma saboda a duniya ba matsalar talaucin da ta kai yunwa. Idan aka yaƙi yunwa da noma, an kori talauci. Manomanmu suna da niyyar noma, amma a ƙarfafa musu guiwa su yi noman shi ne abin da suka rasa.

Tsohon Kwamishinan, wanda ya taɓa zama manajan tsare-tsare na hukumar bunƙasa aikin gona na Jihar Bauchi ya ce, idan har ana so noma ya ci gaba sai gwamnati ta zuba jari mai yawan gaske a harkar, wanda a cikin sa ne za a riƙa yin bincike, jami’o’in da kwalejoji da sauran makarantu da hukumomin da aka kafa da nufin bunƙasa aikin gona za su yi ayyukan da suka kamata.

Za a samar da iri da malaman gona kuma idan manoma suka noma abinci, noman da suka yi zai samar da isashshen abincin da zai jawo ’yan kasuwa da masu masana’antu idan suka zo, suna sayan kayayakin amfanin gonan in ya wadata kamfanoni za su shigo, saboda su sayi amfanin gonan, su sarrafa shi idan suka sarrafa shi za a sami sauƙin talauci da raguwar rashin aikin yi, abinci zai wadata kuma arzikin manoma da mutanen ƙasa zai yalwata.

Ya ce, kuma kamfanonin za su ƙarfafa masana’antu suna samun kayayyakin gona da za su riƙa sarrafawa a fadada su, kamfanonin za su riƙa biyan kudin da za a yi musu bincike kan wata fasahar noma.

Suleiman ya ce, ta hanyar noma ne gwamnati za ta samar da ƙarfafaffen tattalin arziki mai dorewa.

Ya ƙara da cewa, ‘‘bisa la’akari da irin albarkar ƙasa da Allah Ya yi wa Nijeriya, daga Kudu zuwa Arewa ba jihar da ba ta da ƙasar da a kowane lokacin ka yi shuka, shuka za ta tsiro a duk fadin Nijeriya a kowane lokaci ko rani ko damina za a samu abin da aka shuka a ci ko a sayar a samu amfani”.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake tunani ta zuba jari mai ƙarfi, da zai fafado da harkokin noma, kuma ta samar da kayyakin ayyukan gona irin na zamani da iri mai kyau mai inganci da zai ba da yabanya da yawa da ƙwararrun malaman gona da kayayyakin noma kamar taroktoci da injunan casa da kuma hukumomin da za su riƙa sayan amfanin gonan. Idan ta yi haka za a samu mafita mai kyau.