✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin yin albashi ya janyo karancin cinikin raguna a Abuja

Hakan ta sa ragon dubu 200 kwana biyu baya, yanzu ya dawo dubu 150

Farashin raguna ya fadi warwas a kasuwannin Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ’yan kasuwa ke alakanta hakan da rashin yi wa ma’aikata albashin wannan watan.

Aminiya ta gano cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoton da ranar Talata, hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ba su yi wa ma’aikatansu albashin watan Yuni ba.

Hakan dai a cewar ’yan kasuwa ya yi matukar kawo wa kasuwar dabbobin layyar da ke ci shekara-shekara tsaiko a bana.

Malam Mahmuda Bunkure, wani dillalin raguna a titin Kubwa da ke Abuja, ya ce ragon da suke sayarwa Naira dubu 200 kwana biyu da suka wuce, yanzu ya dawo dubu 150.

Ya bayyana hakan da cewa abin tsoro ne la’akari da tsadar dabbobin a wuraren da suka sayo su da kuma kudaden da suka kashe wajen yin jigilarsu zuwa Abuja.

Shi ma wani mai sayar da dabbobin a kasuwar ta wucin gadi, Malam Sulaiman Mu’azu, wanda ya ce ya shafe shekara bakwai yana kai raguna Abuja da Babbar Sallah, ya ce har zuwa yanzu bai ga kwastomominsa da suka saba sayayya a wajensa ba, kuma ya ce hakan ba zai rasa nasaba da rashin yin albashi ba.

Shi ma wani da wakilinmu ya tarar zai sayi rago a kasuwar, Muhammed Kashim, ya ce yakan sayi raguna bakwai a kowacce shekara, amma bana matsin tattalin arziki ya sa ya tsaya a guda biyu kacal.