Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta umarci lamamai su fara yin addu’ar Alkunut a salloli don Allah Ya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
Shugaban JIBWIS na Kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya bayar da umarnin, inda ya ce tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya na bukatar jama’a su koma ga Allah su tuba gare shi.
- Rajistar layin waya: Majalisa ta kara wata biyu
- Sakon Shekau: Sojoji da Fadar Shugaban Kasa sun yi gum
“Shugaban JIBWIS an Kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau ya umarci daukacin limamai su fara yin Alkunut don neman taimakon Allah a kan matsalar tsaro a kasar nan”, inji sanarwar da kungiyar ta fitar.
A makon jiya wasu masallatan Juma’a sun fara gabatar da addu’ar ta Alkunut wadda ake yi idan aka samu bullar annoba ko wata matsala da ta addabi jama’a.