Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ce jagororin Arewan Najeriya sun san hanyoyin da za a magance matsalar tsaro da talauci da yunwa da suka addabi yankin, amma ba su yi a aikace.
Sarkin Musulmi ya shaida wa taron sarakuna da jagororin Arewa cewa yadda matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi da kuma talauci, musamman a tsakanin matasan Arewacin Najeriya, babbar barazana ce ga kasar.
Da yake jawabin da taron da suka gudanar a Kaduna, Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa yanzu ’yan Najeriya a fusace suke, saboda yunwa da talauci, ga kuma “durkushewar harkokin samun kudi da sana’o’i, don haka babu yadda za a yi mu ce komai na tafiya daidai alhadi talauci da rashin tsaro sun addabi jama’a.
“Na sha fada kuma zan kara maimaitawa, al’amura sun dagule a Arewa kuma wajibinmu ne a matsayin sarakuna da ke jagorantar miliyoyin al’ummar Arewa mu nemo mafita.
- Za mu kafa kwamitin ƙayyade farashin kayan abinci — Kashim Shettima
- Sojoji sun gano haramtacciyar masana’antar ƙera makamai a Filato
- Matasa sun yi zanga-zanga saboda tsadar rayuwa a Sakkwato
“Kuma, ba wai ba mafitar ba ce babu, amma abin da ya dace ne ba ma yi, saboda duk lokacin da muka zauna irin wannan taro, kowa na kawo shawarwari masu kyau, amma kowannenmu a cikin dakin taro muke watsar da abin da shawarwarin.”
“Shi ya sa a karon muka gayyato kungiyar dattawan Arewa da saurasu domin ganin yadda za a magance matsalolin Arewa da ma kasar nan a aikace; Ga bangaren ilimi, ga na lafiya su ma sunan nan baya ga talauci da rashin tsaron,” in ji Sarkin Musulmi.
A nasa jawabin, gwamnan Kaduna, Uba Sani bisa wakilcin mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe, ta ce samun tsaro babban ginshiki ne wajen samun ci gaban Arewa.
Don haka ida so muke a sami ci gaban tattalin arziki, wajibi ne mu san na yi wajen kawo karshen garkuwa da mutane da sauran nau’ikan ta’addanci da suka zama ruwan dare a yankin.
Uba Sani na ganin mafita ita ce hada kai a tsakanin al’umma da shugabanni da gwamnonin Arewa wajen magance matsalolin da ke hana wa yankin cigaba; musamman kafa cibiyar tsaro ta bai-daya domin yaki da ta’adanci.
A bangarensa, shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi, wanda daraktan hukumar na jihar Kaduna, Abdul Enenche, ya waklita ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen dakile barazanar tsaro dun kafin a aikata su.
Jami’in, wanda ya bukaci hadin kai wajen yakar miyagu, ya kuma bayya cewa masu ba wa bata-gari bayanai babbar matsala ce da ke bukatar magancewa da hadin kan masu ruwa da tsaki.