Majalisasr Malamai ta Jihar Kano da hadin gwiwar Gamayyar kungiyoyin Arewa ta CNG sun kaddamar da addu’o’i na musamman a fadin Arewacin Najeriya domin neman Allah Ya kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar yankin.
Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya ce a yayin addu’o’in na musamman, za a yi ta rokon Allah Ya ba wa jami’an tsaro nasara a yakin da suke yi da ’yan Boko Haram da ’yan bindiga da sauran bata-gari a ko’ina a fadin Najeriya.
“Manyan malamai da alarammomi sun halarci taron inda ake rokon Allah Ya ba sojojin Najeriya nasara a yakin da suke yi domin samar da tsaro da aminci a kasar nan.
“Ana kuma rokon Allah Ya kare ’yan Najeriya, Ya fito da wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane lafiya, Ya kuma kawo cikakken kwanciyar hankali da fahimtar juna da zaman lafiya a Arewa da ma Najeriya baki daya.
“Za a ci gaba da waddannan addu’o’i a kowace ranar Juma’a a fadin Arewacin Najeriya, har sai an samu nasara,” inji sanarwar da Suleiman ya fitar a Abuja.
An kaddamar da taron addu’o’in na musamman ne a Masallacin Alasan Dantata da ke unguwar Koki a Jihar Kano, karkashin jagoranciin Shugaban Kungiyar Alarammomi ta Najeriya, Imam Gwani Alyu Saleh da Shugaban CNG na Kasa, Balarabe Rufai.