Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi su rubanya addu’o’i a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan domin samun tsaro da aminci a Najeriya.
Sarkin Musulmin kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ya bukaci ’yan Najeriya da su zama masu lura a yankunansu game da matsalar tsaro da ke addabar kasar.
- An kama dan bindiga ya kai hari a masallaci
- Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’
- Shugabannin Tsaro na ganawar sirri da Majalisar Tarayya
“Su yawaita yin HasbunaLlahu wani’mal wakeel; Astagfirullah; La hawla walakuwata ilabiLlahi-l-Aliyi-l-Azeem; La ilaha illa anta Subuhanaka inikuntu mina zalimeen, Allah Ya kawo wa kasar sauki.
“Majalisar na kuma kira ga Musulmi su mara wa duk yunkurin tabbatar da dorewar Najeriya a matsayin kasa day dunkulalliya baya,” inji sakon da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar.
Sarkin Musulmi ya jaddada muhimmancin ’yan kasa su rika taimaka wa hukumomin tsaro domin magance matsalar da ta zama ruwan dare.
Ya yi kiran ne yayin nuna damuwa game da yadda rashin tsaro ya haifar da kashe-kashe da kuma tsoro, zullumi, rudani, da a zukatan ’yan Najeriya.
Don haka, Sanarwar ta da Mataimakin Babban Sakataren Majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya fitar ta bukaci “gwamnati a dukkannin matakai su ninka kokarin da take yi wurin tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar.”