✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsari shi ne kalubalen tattalin arzikin Najeriya – Dokta Nazifi

Fitaccen masanin tattalin arziki, Dokta Nazifi Abdullahi Darma, ya ce, rashin tsarin tattalin arziki mai dorewa shi ne babban kalubalen da ke kawo tarnaki dangane…

Fitaccen masanin tattalin arziki, Dokta Nazifi Abdullahi Darma, ya ce, rashin tsarin tattalin arziki mai dorewa shi ne babban kalubalen da ke kawo tarnaki dangane da bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
Dokta Nazifi wanda babban malami ne da ke koyarwa a sashen tsimi da tanadi a Jami’ar Abuja, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja a karshen makon jiya .
Ya ce, kasashe masu tasowa kamar kasar Indiya da Brazil da Malesiya da Singapore da sauransu sun sami bunkasar tattalin arzikinsu ne saboda tsari da suke da shi a tattalin arzikinsu.
Ya ci gaba da cewa wadannan kasashe a duk shekaru biyar sai sun tsara yadda za su cimma manufofinsu ta hanyar la’akari da kowane bangaren tattalin arzikinsu da hasashe da kuma kudin da za su kashe.
Ya bayyana cewa ba wai wayar gari suke yi ba su bayyana kasafin kudi tare da tunkarar matsalolin tattalin arzi kamar yadda muke yi a Najeriya.
Ya kara da cewa sai sun san matsalolin da za su fuskanta tare da yadda za su magance su da kuma adadin kudin da za su kashe.
Saboda haka ya ce muddin kasa ta gano matsalolinta da kudin da za ta kashe to samar da ginshiki ga masu zuba hannun jari za su hada karfi da ita don su yi maganin matsalolin bunkasar tattalin arziki.
“Amma mu a nan Najeriya ba haka ake yi ba. Ba mu da tsarin tattalin arziki na bai daya. Tsarin da muke da shi tuni aka yi fatali da shi tun a shekarar 2005. Ma’aikatar tsare-tsare ta kasa a shekarar 2009/2010 ta fitar da tsari da suka yi wa lakabi da burin shekarar 2020 daga cikinsa ne suka fitar da tsari na karamin zango, amma abin takaici ba a yi amfani da shi ba. Wannan ita ce matsalarmu kuma shi ne kalubalen da muke fuskanta a karsar nan,” inji shi.
A karshe ya ce dole sai Najeriya ta gano matsalolinta a kowane fanni tare da sannin kudin da za ta kashe sannan kuma ta tsara yadda za ta kashe kudinta sannan tattalin arzikinta zai bunkasa.