✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin tsaftataccen ruwa: ’Yan Najeriya miliyan 60 na iya kamuwa da cututtuka

A cewarsa, hanyoyin mafitsara da hanji za su iya kamuwa da cututtukan da suka hada da ciwon mara, gudawa, tsargiya da dai sauransu.

A daidai lokacin da ake bikin ranar ruwa ta duniya, likitoci sun yi gargadin cewa miliyoyin ’yan Najeriya da basu da hanyoyin samun tsaftataccen ruwan shan ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka daban-daban.

Alkaluma daga hukumomi daban-daban, ciki har da Ma’aikatar Ruwa ta Tarayya sun nuna cewa akwai sama da ’yan Najeriya miliyan 60 da har yanzu ba sa iya samun tsaftataccen ruwan sha a kullum.

Ministan Ruwa, Injiniya Sulaiman Adamu ya sha nanatawa a lokuta da dama cewa samar da ruwan sha alhaki ne da ya rataya a wuyan jihohi, ko da yake masu ruwa da tsaki da dama na ganin cewa gwamnatoci ba su yi abin da ya kamata ba wajen magance kalubalen.

Sai dai masana harkar lafiya na gargadin cewa za a ci gaba fuskantar cututtuka masu alaka da rashin tsaftataccen ruwan sha, musamman a yankunan karkara muddin ba a tashi tsaye wajen magance matsalar ba.

Wasu mutane na dibar ruwa a kududdufi

Dakta Clement E. na asibitin Bolpraize dake Garam a jihar Neja ya yi gargadin cewa mutanen da ke dibar ruwan sha  daga kududdufai na fama da cututtuka da dama masu alaka da kwayoyin cuta ke haifarwa.

A cewarsa, hanyoyin mafitsara da hanji za su iya kamuwa da cututtukan da suka hada da ciwon mara, gudawa, tsargiya da dai sauransu.

Kazalika, likitan ya kuma ce hatta masu dibar ruwa daga koguna su ma ba su tsira ba saboda za su iya kamuwa da cutar amai da gudawa wacce ke iya yaduwa kuma ta kai ga asarar rayuka.

Haka rijiyoyin birtsatse barkatai na da matukar hatsari – Masani

Wani masanin Ilimin Muhalli a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Dakta Yusuf. I. Garba ya ce yawan haka rijiyoyin birtsatsen barkatai kan rage yawan ruwan da ke karkashin kasa.

A tattaunawarsa da Aminiya, Dakta Yusuf wanda Malami ne a Sashen Kimiyyar Muhalli na jami’ar ta Bayero ya ce, “Ruwan dake karkashin kasa yana taruwa ne kamar yadda na kududdufi yake. To idan ana yawan haka birtsatse, ya danganta da yawan ruwan wurin, ya kan sa yawan ruwan ya yi kasa sosai.

“To yawan hakawar yana sa yawan ruwan ya yi kasa ko ma ya kare gaba daya. Kamar a wasu unguwannin da ake yawan hakawa za ka ga cewa in ka haka karamin birtsatsen ba za ka sami ruwa ba.

“Abin da ya kamata a rika yi shine gina madatsun ruwa a maimakon yawan haka rijiyoyin na birtsatse,” inji shi.