✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Rashin sani ke sa mutane sukar aikin layin dogo daga Kano zuwa Nijar’

“Hatta jikokinmu sai sun ci gajiyarsa, ba wai abu ne na sha yanzu magani yanzu ba."

Fitaccen dan kasuwar nan na Kano kuma shugaban rukunin kantunan Jifatu, Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya ya ce rashin sani ne ke sa wasu mutane sukar aikin shimfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Ya ce idan aka kammala, aikin zai taimaka wajen farfado da tarihin sama da shekaru 1,000 na ciniki tsakanin kasashen yankin Sahara.

Dan kasuwar, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ’yan jarida a Kano ranar Asabar ya kuma ce aikin zai bunkasa tattalin arzikin Najeriya a daidai lokacin da yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba ta Afirka (AfCFTA) ta fara aiki.

Ya kara da cewa, “Dukkan wani mai ilimi da mai hangen nesa ya dade yana jiran wannan ranar da tarihin ciniki tsakanin kasashen yankin Sahara zai farfado.

“Saboda haka muna godiya ga Shugaban Kasa saboda kaddamar da wannan aikin Wada zai bi ta jihohin Kano da Jigawa da Katsina sannan ya dangana da Maradi.

Shugaban Rukunin Kantunan Jifatu, Alhaji Sabitu Muhammad Yahaya

“Mu ’yan kasuwa mun fi kowa sanin amfanin wannan aikin. Ina tina lokacin da ake kawo kaya kai tsaye tun daga Arlit har zuwa Kano.

“Ina matukar mamaki yadda wasu suke sukar Shugaban Kasa a kan wannan aikin.

“Lokacin da marigayi Shugaba Shagari ya kaddamar da aikin titin kan iyaka na Seme a Jihar Legas har ya dangana da Jamhuriyar Benin, akwai wani dan Arewa da ya ce uffan a wancan lokacin? Me ya sa sai a kan wannan za a yi ta cece-kuce?

“Wannan wani gagarumin aiki ne da hatta jikokinmu sai sun ci gajiyarsa, ba wai abu ne na sha yanzu magani yanzu ba, tunani ne na shekaru 70 zuwa 100 masu zuwa.

“Ina da kwarin gwiwar za a kammala wannan aikin kamar yadda aka tsara Insha Allahu.

“Ya kamata ’yan kasuwarmu da ’yan siyasa da masu iliminmu su kalli wannan aikin a matsayin nasu kuma su bayar da gudummawa wajen ganin ya kai ga gaci.

“Yanzu alal misali idan mutum ya dauki yalo daga Daura ya kai Fatakwal, ko ya dauki doya daga Warri ya kai ta Aljeriya, ko ganyen shayi daga Sudan ya kai shi Fatakwal, ba a samu ci gaba ba?

“Wannan fa shine kasuwanci tsakanin kasashen Saharar da muke magana a kai,” inji Alhaji Sabitu.

Dan kasuwar ya kuma yi hasashen cewa idan aka kammala, hatta darajar filaye da kadarorin yankunan da aikin zai shafa sai ta ninka kamar sau 10.

A ranar Talatar da ta gabata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida layin dogon mai tsawon kilomita 300 ta bidiyo, wanda kuma ake sa ran kammala shi nan da 2023.