✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin sani

Wani dan A Daidaita Sahu ne ya dauko wata mata daga Rijiyar Zaki zuwa kofar Mata. Ta ci kwalliya sosai, suna cikin tafiya sai wata…

Wani dan A Daidaita Sahu ne ya dauko wata mata daga Rijiyar Zaki zuwa kofar Mata. Ta ci kwalliya sosai, suna cikin tafiya sai wata mata ta tsaida shi, sai matar nan ta ce, a’a, kar ya dauki kowa, ita dirof ta dauka. Ya wuce ya kai ta har inda za ta sauka. Da ta sauka ya ga za ta wuce, ya ce: “Ba ki ba ni kudin ba.” Sai ta matso kusa da shi ta cusa masa zagi. Har ya buda baki zai yi magana, sai wani mutum da ke wucewa ya ce masa ya yi shiru, domin ba ta da hankali.

Daga Ibrahim Hamisu Kano, 08188966748