dan kwallon kulob din FC Barcelona na Sifen Lionel Messi ya ce sayar da Cristiano Ronaldo da Real Madrid ta yi ya sanya kulob din ya zama bai da karfin ’yan kwallo kamar da.
A lokacin da ake hira da Messi a gidan rediyon Catalunya na Sifen a shekaranjiya Laraba, ya ce a gaskiya yanzu kulob din Real Madrid sai a hankali, ganin yadda suka rabu da Cristiano Ronaldo.
Messi ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ’yan kwallon FC Barcelona su yi kokarin ganin sun lashe kofin Zakarun Kulob na Turai a gaba, ganin da wuya kulob din Madrid ya iya lashe kofin a wannan karo saboda rashin Ronaldo.
Sai dai Messi ya ce yanzu kallo ya koma kan kulob din Jubentus ne, wurin da Ronaldo ya koma kuma mai tattare da zaratan ’yan kwallo.
Cristiano Ronaldo, wanda ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi yawan zura kwallaye a raga a kulob din Madrid, ya canja sheka zuwa kulob din Jubentus na Italiya ne a kan Fam miliyan 100. Yana daga cikin ’yan kwallo uku da za su fafata a gasar Gwarzon dan kwallon Duniya ta bana a Ingila a ranar 24 ga wannan wata da muke ciki.
Kawo yanzu kulob din Madrid ya lashe wasanni uku da ya yi a gasar La-Liga kuma shi ne na biyu a teburin gasar, da hakan ya nuna kulob din bai yi kewar rabuwa da Ronaldo ba kamar yadda wadansu suka yi tsammani.