✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin ofishin jakadanci na ci mana tuwo a kwarya – ’Yan Najeriya mazauna Bangladesh

Sun ce duk abin da ya taso, sai dai su tuntubi ofishin jakadancin da ke Indiya

Akwai ’yan Najeriya mazauna kasar Bangladesh birjik wadanda suka shiga kasar saboda dalilai mabambanta. Aminiya ta samu zantawa da sakataren kungiyar ’yan Najeriya mazauna kasar, Injiniya Usman Mohammad Tomsu, wanda ya bayyana yanayin rayuwar ’yan Najeriya ke ciki a can. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Yaya rayuwa da mu’amalar ku ’yan Najeriya mazauna Bangladesh take?

Yanayin rayuwa da mu’amalarmu tsakanin mu ’yan Najeriya da ’yan kasar Bangladesh, babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah (SWT). Saboda babu wata matsala a tsakaninmu da su, in ma akwai ba ta wuce ta bambancin harshe ba.

Yaya mu’amalarku take da ofishin jakadancin Najeriya a kasar?

Gaskiya akwai matsala. Da farko babu ofishin jakadancin Najeriya a Bangladesh sai dai a Indiya. Na biyu, akwai rashin tsayayyun hanyoyin da ya kamata mu rika amfani da su wajen mika koke-kokenmu a ofishin jakadancin Najeriya da ke Indiya.

Galibinmu ba su ma san yadda za su yi su tuntubi ofishin jakadancin ba. Fatanmu a samar da wani tsari wanda zai taimaka mana wajen saukin isar da sakonni da kuma tuntubar ofishin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ko kuma in so samu ne, ofishin jakadancin na Indiya ya taimaka ya bude mana wani karamin ofishinsa a nan Bangladesh inda za mu rika kai bukatunmu, in ya so daga nan sai a dauka zuwa babban ofishinsa da ke Indiya.

Wadanne irin kalubale kuke fuskanta?

Kamar yadda na bayyana a baya, ba mu da wani kalubale da ya wuce wahalar da mukan sha kafin mu iya mika kokenmu ga ofishin jakadancin Najeriya da ke Indiya kasancewar babu makamancinsa a Bangladesh, dole sai mun dagana da Indiya.

Mene ne ya fi wahalar da ke a zaman kasar?

Wahala kam ba a rasa ba, musamman yadda wasu lokuta idan ma’aikata ko mahukuntar kasar suka tashi hukunta wani mai laifi sai ka ga abin ya shafi har da wanda bai san hawa ba balle sauka.
Haka nan, idan mutum yana neman gurbin karatu a kasar yakan dade kafin ya samu bizarsa.

Sannan wadanda ke cikin kasar, misali dalibai, suna wahala wajen cire kudi a banki saboda Dala 20 kacal Gwamnatin Najeriya ta ba su damar cirewa kowane wata wanda kudin ba zai ishi mutum sayen abincin mako daya ba balle kuma ya iya biyan kudin makwancinsa da kudin makaranta da sauransu. Kuma yakan dauke su lokaci mai yawa idan suka tafi cire kudi a banki.

Yaya kuke fama da batun abinci?

Gaskiya batun abinci akwai sauki sosai a nan, babu tsada. Ka san da yake mu ’yan Najeriya duk inda muka je mukan yi kokarin sabo da yanayin abincin al’ummar wurin. Kamar a nan, akwai abinci irin su ‘chiken biriyani’ da sauransu. Haka nan, akwai kayan marmari a wadace.

Batun addini kuma fa?

Alhamdu lillahi, babu abin da za mu ce saboda ana bai wa kowa damar gudanar da addininsa ba tare da wata tsangwama ba. Idan kai Musulmi ne, akwai masallatai da dama, kowace unguwa ba ta rasa masallatai akalla guda uku ko ma fiye da haka. A ganina babu kasar da ta kai Bangladesh yawan masallatai. Haka su ma Kiristoci, suna da wurin bautarsu, wato coci-coci.

Mene ne ya fi burgewa game da zaman kasar?

Yanayin harkokikin kasuwancinsu da al’adunsu da makarantunsu da tsarin karatunsu, duk abun burgewa ne. Wasunmu ma suna da masana’antu a nan saboda saukin sha’anin kasuwanci a kasar.

Ko kana da wani kira ga gwamnatin Najeriya?

Kwarai kuwa. Muna da bukatar gwamnati ta shigo ta maganace mana matsalolin da muke fuskanta, wanda mu da kanmu ba za mu iya magance su ba, dole sai gwamnati. Sai ka ga mutum ya shafe kwanaki a filin jirgi wai ana duba takardunsa, ko kuma a ce ana jiran bayanai daga Gwamnatin Najeriya. Hakan ya faru da mutanenmu da dama, sai dai mu ce Allah ya kare mu baki daya.