Hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki a Najeriya FCCPC ta ba ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa wajen haddasa tsadar kayayyaki wa’adin wata guda su karya farashin kaya.
Sabon mataimakin shugaban hukumar FCCPC da aka naɗa, Mista Tunji Bello ne ya bayyana haka a wani taron yini ɗaya da masu ruwa da tsaki suka yi kan ƙazamar ribar ‘yan kasuwa ke samu.
Cikin sanarwar da ya bayyana a ranar Alhamis a Abuja, Bello ya ce hukumar za ta fara aiki bayan cikar wa’adin.
Ya ce taron an yi shi ne don magance ƙaruwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma mugun hali na ƙungiyoyin ‘yan kasuwa.
Bello ya yi bayanin yadda Hukumar ta gano cewa ana siyar da injin markaɗa kayan marmari da aka fi sani da Ninja a wani babban kanti da ke Texas akan dala $89 kwatankwacin Naira dubu ɗari 140, amma an baje wannan samfurin akan kuɗi Naira dubu 944, da ɗari 9 da 99.00 a wani babban kanti da ke Victoria Island a Legas.
Bello ya yi mamakin dalilin tashin farashin gwauron zabin da ake amu ba bisa ƙa’ida ba idan aka kwatanta da lamarin a Jihar Texas ta Amurka.
Ya ce ƙaruwar farashin da ba su dace ba, da suka haɗa da ƙayyade farashin na yin barazana ga zaman lafiyar tattalin arzikin ƙasar.
“A ƙarƙashin sashe na 155, masu karya dokar ko dai ɗaiɗaikun mutane ko kamfanoni na iya fuskantar hukunci mai tsanani da suka haɗa da tara da ɗauri idan kotu ta same su da laifin.
“Za mu yi hakan ne domin daƙile duk wani ɓangare da ke cikin irin wannan haramtattun ayyuka.
“Duk da haka, umarnin a yau bai da hukunci, amma muna ina kira ga masu ruwa da tsaki da su rungumi kishin ƙasa da haɗin kai.
“A cikin wannan umarnin ne muke ba da wa’adin wata ɗaya (Satumba) kafin Hukumar ta fara tabbatar da hukuncin,” in ji shi.
Bello ya ce gwamnati na sane da yawancin matsalolin da manyan kasuwar ke fuskanta.