Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya ce babu gwamnatin da ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya a tarihi tamkar ta tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo.
El-Rufai ya ce alkalumma sun tabbatar da yadda aka samu bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi da rage hauhawar farashi a wa’adi na biyu na mulkin Obasanjo.
Obasanjo dai shi ne Shugaban Najeriya na farko a tsarin dimokuradiyya wanda ya jagoranci kasar tsawon wa’adi biyu daga 1999 zuwa 2007 a jamhuriya ta hudu.
- Birtaniya ta kara kudin bizar dalibai da masu yawon bude ido
- Burkina Faso ta bai wa jami’in sojin Faransa wa’adin ficewa daga kasar
El-Rufai, wanda ya rike kujerar Ministan Abuja a gwamnatin ta Obasanjo, ya ce Najeriya wadda ita ce kasa mafi yawan al’umma a nahiyyar Afirka, ta samu yalwar tattalin arziki daga shekarar 2003 zuwa 2007.
Tsohon gwamnan ya ce a wancan lokaci, Najeriya ta daidaita a kan turbar tsare-tsare masu inganci kuma ta dace da sa’a a lokacin.
Aminiya ta ruwaito cewa, El-Rufai ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin gabatar da jawabi a taron tasirin nahiyyar Afirka a duniya da aka gudanar a birnin Stellenbosch da ke Afirka ta Kudu.
A yayin taron, El-Rufai ya jaddada muhimmancin nagartattun tsare-tsare da zai taimaka wa kowacce kasa ta fuskar inganta tattalin arziki.
“Muna da Hukumar Tsare-Tsare a Najeriya amma ba ta da wani tasiri sosai.
“Idan aka dubi yanayin tattalin arzikin Najeriya, lokacin da kasar ta fi samun nasara ta fuskar ci gaba da samar da ayyukan yi da rage hauhawar farashi, a shekaru hudu zuwa biyar, shi ne wa’adi na biyu na mulkin Shugaba Obasanjo daga shekarar 2003 zuwa 2007.
“A wannan lokaci wanda shi ne karon farko, Najeriya ta daidaita a kan turbar tsare-tsare sannan kuma mun taki sa’a sosai a lokacin.
“Farashin man fetur ya tashi amma bayan ya fara sauka ba mu ji tasirin hakan ba saboda mun tanadi tsare-tsare.
“A haka muka sauke nauyi wajen biyan duk wasu basussukan kasashen waje da suka rataya a wuyanmu.
“Saboda haka ko da aka shiga matsi na tattalin arzikin duniya a shekarar 2008, ba mu ji wani radadi ba,” a cewar El-Rufai.