✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin lafiya ya hana limamin Masallacin Harami karasa Sallar Juma’a

Sheikh Al Sudais ne ya karasa jagorantar sallar, bayan Sheikh Maher ya gaza ci gaba saboda rashin lafiyar.

Shafin Haramain Sharifain ya rawaito cewa rashin lafiya ya sanya limamin Masallacin Haramin Makkah, Sheikh Maher Muaikili gaza karasa jagorancin Sallar Juma’a da ya fara.

Babban Limamin Masallatan Harami Sheikh Abdurrahman Al Sudais ne ya karasa jagorantar sallar, bayan Sheikh Maher ya gaza ci gaba saboda rashin lafiyar.

A bidiyo da shafin ya wallafa a dandalin sada zumunta an ji muryar malamin yana tsaka da karatun fatiha, sai kuma aka ji shiru muryarsa ta dauke.

Jim kadan sai aka ji Sheikh Sudais ya karbi ragamar jagorancin sallar ya karasa karatun Fatiha har zuwa idar da sallar.

Sai dai daga baya shafin ya wallafa cewa an kai Sheikh Maher cibiyar kula da lafiya kuma likitoci sun tabbatar cewa ya samu sauki, amma ba zai iya ci gaba da jagorancin sallar ba.