✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin kulawar gwamnati ya jawo wa nakasassu talauci – Dokta Awais

Wani malami a tsangayar Kimiyyar Halayyar dan Adam a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dokta Muhamamd Awais ya ce rashin kulawar gwamnati ne ummulhaba’isin haifar…

Wani malami a tsangayar Kimiyyar Halayyar dan Adam a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dokta Muhamamd Awais ya ce rashin kulawar gwamnati ne ummulhaba’isin haifar da talauci a tsakanin nakasassun kasar nan.
Dokta Awaisu ya bayyana haka ne a wurin taron neman mafita ga rayuwar nakasassun nan da Jami’ar Bayero ta gudanar a karshen makon jiya, inda ya ce “Rashin kulawar gwamnati a Najeriya ta jawo idan nakasa ta samu mutum sai talauci ya baibiye shi, kuma idan talaka ne shi shi ke nan ya tashi daga aiki. Idan muka dubi mutanen nan suna da iyali da suke bukatar kulawarsu, to ba su samu tallafi ba, ta yaya za su taimaki iyalansu?”
Ya ce kasashen da suka ci gaba suna da kyakkyawan tsarin tallafa wa nakasassu, inda hakan ya sanya rayuwarsu a take cikin sutura ba kamar Najeriya ba inda suke dogara da bara ba.
Dokta Awaisu ya yi kira ga gwamanti ta hanzarta sanya hannu kan kudirin dokar da tun lokacin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo aka mika ta domin kyautata rayuwar nakasassu, amma ya ki sanya mata hannu. Haka Jonatahan bai sa mata hannu ba. “Muna fatan Shugaba Buhari zai sanya hannu a kan dokar tare da aiwatar da ita, don ba wa nakasassun kasar nan kular da suke bukata; da ta hada da samun ilimi da kiwon lafiya da sauran bukatun da suka zama
wajibi kowane dan kasa ya samu,” inji shi.
A mukalar wani malamin Jami’ar Maiduguri, Mista Adetunj Yunus ya gabatar ya ce akwai bukatar gwamnati da kamfanoni su tsara gine-ginensu yadda nakasassuza su iya shiga ba tare da matsala ba. “Wadanann gine-gine sun hada da makarantu da asibitoci da sauransu da suka zama wajibi dan Adam ya samu,”  inji shi.
Tunda farko a jawabin Shugaban Kwamitin shirya taron Dokta Rufa’i Ahmad Yusuf ya ce sun shirya taron ne don lalubo hanyoyin fitar da nakasassu daga kuncin da suke ciki a kasar nan.
“Muna so mu ga sun yi rayuwa kamar kowane dan Adam. Wannan nakasa da suke tare da ita, kowane daya daga cikinmu zai iya samun kansa da ita. Don haka akwai bukatar a tallafa wa rayuwarsu ba kawai ta hanyar ba su sadaka ba, har ta hanyar ba su hakkinsu a matsayinsu na ’yan kasa,” inji shi.