Biyo bayan wata ‘yar kididdiga, na fahimci cewa daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo farin jini kangararre shi ne: kwarewar mutum wajen yin Turanci mai kayatarwa da kuma iya fayyace al’amura masu sarkakiya da tankiya game da addini. Ita wannan ka’ida, in za a yi mata adalci, za a ce tana da firgitarwa. In kuma za a mata zato na ba-sani-ba-sabo, za a ce wauta ce; dalili kuwa shi ne: suna kara raba akidun mutanen Arewa ne. Babban burin irin wadannan mutane a kafar Facebook ba komai ba ne illa, watakila, sukar akidun wasu da ba nasu ba. Wannan abin takaici ne. Ina mai jin haushin cewa irin wannan babu inda zai kai mu.
Manyan matsalolin Arewa – kai har ma Najeriyar – su ne: cin hanci, ilimi (musamman na ‘ya mace), kiwon lafiya, tsaro da kuma aikin yi. A da, nakan kasa gane tasirin abin da muke rubutawa a nan, amma ban da yanzu. Mafi yawan matasa maza da mata suna kaunarmu ne – duk da cewa mu ma matasan ne – saboda zaburar da su, da koyar da su wasu al’amura da muke yi, da sauransu. Irin yabo da suka, da mutum ke samu bayan rubuta wani abu, na fayyace abubuwa da dama game da wadanda muke sadarwa da su.
A makon da ya gabata, na dora wasu hotuna da na dauka a daya daga masallatai mafiya kyau a duniya, wanda abin mamaki, a Köln, Jamus yake. A fakaice, na yaba wa Turawa a kan wannan saboda kawaicinsu da hakurinsu ga wasunsu. Wasu a nan suna ganin yin hakan kuskure ne. Amma babu makawa mu kam ba mu da kawaici da hakuri ga junanmu. Kar ka je da nisa, har Turai; duba inda kake domin gaskata wannan magana tawa. Alal misali, a mako guda, an samu husuma kan mallakar wasu masallatai biyu tsakanin Malam Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu mutane a Kano. Ba don wani ikon Allah ba, da an zubar da jini. Wannan tsakaninmu Musulmi fa ke nan! Ban taba jin irin wannan tsakanin Kiristocin Najeriya ba – ban kuma ce ba sa yi ba.
Ba shakka ‘yan Najeriya – Musulmi da Kiristoci – ba mu da hakuri da junanmu sosai. Duk da haka, husuma tsakanin Musulmi abin kunya ne. Kamar yadda na fayyace, ban taba ganin rubutu [a Facebook] ba, wanda ‘yan “Catholics” suke dora kaulasan a kan ‘yan “Witness Apostles”; ko kuma “Pentacostals” na cin fuskar “Anglicans”, da dai sauransu.
A daya bangaren, yana da wuya a wuni ba ka ga wani Sufi yana cin fuskar Wahabiyawa ba, ko kuma dan Shi’a yana tsine wa Ahlussunah ba; haka ma, za ka ga Wahabiyawa na cin fuskar Sufaye ko Ahlussunah na tsine wa ‘yan Shi’a. Wasu na yin hakan ne ba dare ba rana, amma saboda munafunci, sai ka ga wai irin wadannan mutane suna kira kan hadin kan Musulmi, ci gaban Arewa ko kuma wai a daina son kai. In dai a haka za a ci gaba, to hadin kan Arewa zai zama tatsuniya ce kawai; a haka za mu dunkule; kuma tsarin daga-su- sai-’ya’yansu zai ci gaba da hayayyafa yayin da kowa ba zai taimaki kowa ba sai ‘yan akidarsu.
Kamar yadda na taba bayyanawa, na sha yanke huldata da irin wadannan ja’irai da ba sa barin wasu a kan ra’ayinsu, ba don ba zan iya jure wa hakan ba, sai don zaman lafiya da hadin kai. Ban taba boye cewa na fi karkata ta farkin Sunnah ba fiye da kowace akida, amma na yi amanna da darajar dan Adam da kuma ‘yancin ra’ayinsa. Na yi zama na lumana da Hindawa da Sikawa, da Kiristoci, kai har ma da wadanda ba su yarda akwai Ubangiji ba. Kyakkawan misali shi ne: matar da nake haya a gidanta – Kirista ce, kuma farar Bajamushiya – takan wanke min kaya, ta dafa mana abinci ta kuma share min daki tun da na zo nan. Ba a taba tsangwamata saboda addinina ba. Labarin daya ne da zuwana Indiya ma – inda na yi shekara biyu (2013-2015). Sirrin haka kuwa ba komai ba ne illa yadda muke mutunta akidun juna. A Alkur’ani, sura ta 109 cewa ta yi: “Ku yi addininku , na yi nawa”, shi ke nan!
Don Allah, ka zamo mai wanzar da Salama a farfajiyarka [ta Facebook], a gidanka, a wurin aikinka da kasuwanninmu. Ka fahimci cewa: duk yadda ka yi, ba za ka iya tursasa kowa ya bi akidarka da addininka ko salon rayuwarka ba. Muna da bambanci. Ba za mu taba zama daya ba. Haka Mahalicci yake son ganinmu; ba za ka iya canjawa ba; abin ba sauki; kuma ba zai yiwu ba. Ma’ana: kokarin yin haka tamkar bata lokaci ne – ya ma fi haka muni.
Muhammad Sabi’u ne ya fassara wanna makalar da Muhsin Ibrahim ya rubuta da harshen Turanci.