✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin hanyoyi da ruwan sha ne manyan matsalolin yankin Lame – Bala Rishi

Zababben dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Lame da ke Karamar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdu Rishi ya ce rashin…

Zababben dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Lame da ke Karamar Hukumar Toro, a Jihar Bauchi, Alhaji Bala Abdu Rishi ya ce rashin hanyoyin mota da ruwan sha ne manyan matsalolin da suke damun al’ummar mazabarsa. Alhaji Bala Abdu Rishi ya bayyana haka ne a lokacin yake zanta wa da Aminiya.

Ya ce don haka abubuwan  da zai mayar da hankali a kai ke nan, da zarar an rantsar da su a majalisa.

Bala Rishi ya ce babban burinsa shi ne ya kyautata wa al’ummar mazabar musamman ganin irin karramawar da suka yi masa, wajen zabensa a matsayin wakilinsu a Majalisar Dokokin  Jihar Bauchi.

“Al’ummar wannan mazaba ne suka bukaci in fito wannan takara. Kuma su ne suka dauki nauyin wannan takara, saboda zaman lafiyar da ke tsakanina da su, don haka dole in tashi tsaye wajen ganin na kyautata musu,” inji shi.

Ya yi kira ga al’ummar mazabar kan su ci gaba da ba shi goyon baya da hadin kai, domin ganin ya cimma kudurorin da ya sanya a gaba.