✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin hanya na damun mutanen yankin Jibiya

Al’ummar garuruwan Tankuri da Gangara da Kukar Babangida da Daddara a Karamar Hukumar Jibiya sun koka kan rashin hanya da za ta saukkaka musu harkokin…

Al’ummar garuruwan Tankuri da Gangara da Kukar Babangida da Daddara a Karamar Hukumar Jibiya sun koka kan rashin hanya da za ta saukkaka musu harkokin rayuwa kamar sauran yankuna.

Mai magana da yawun mutanen garin Tankuri, Alhaji Ashiru Tankuri ya shaida wa Aminiya cewa “Daga bakin garin ’Yammaiwa da ke titin zuwa Batsari hanyar ta fara, ta shiga garin Tankuri zuwa Gangara ta bulle Kukar Babangida ko Daddara dukkansu a kan babban titin zuwa Jibiya. Idan aka yi hanyar za ta hada kananan hukumomin Batagarawa da Batsari da Jibiya. Kuma za ta bayar da dama ga ’yan kasuwa da manoman yankuna da dama samun saukin kai kayansu kasuwa.”

Ya cewa, “Yanzu in lalurar  zuwa hedkwatar Karamar Hukumar Jibiya ta kama mu sai mun bi ta Katsina ko Batsari mu kai. Maimakon tafiyar minti 30 sai mun dauki awa 2 zuwa 3 kafin mu je.”

Alhaji Ashiru ya ce maganar ruwan sha ko wajen shan magani ballantana babbar makaranta a yankin ba sa yin su dalilin rashin hanya, wadda ya ce in damina ta zo su ne suke aikin gayya su cike ramukan da ake samu.

“Yanzu haka in mutun zai bi hanyar gabansa na faduwa saboda bai san ramin da zai tarar ba. Wannan ita ce babbar matsalarmu a wannan yanki. Duk kayan noma na rani da damuna babu wanda ba ma nomawa, kuma ana samun kudin shiga daga wajenmu. An yi mana alkawura da dama, amma har yanzu shiru. Yaranmu na son yin kasuwanci da sana’o’i amma  matsalar hanya ta hana mu ci gaba.

Saboda haka muke kira ga Gwamna Masari domin aikin ya fi karfin karamar hukuma ya tuna alkawarin da ya yi mana kafin hawansa na farko kan fitar da mu daga cikin wannan matsala,” inji shi.

Su kuwa al’ummar Unguwar Tudun Katsira da ke garin Katsina kokawa suka yi kan matsalar gadar da ta raba su da makwabtansu da ke Unguwar Dutsin Amare da sauran makwabta. “Ga mu ga Dutsin Amare da Kofar Durbi, amma da zarar an ce ruwan sama ya sauka, shi ke nan mun zama tamkar a akurkin kaji domin hanyar ke nan da  muke amfani da ita, ko babur biyu ba su iya hawa tare. Idan aka samu lalurar rashin lafiya, sai dai mu dauki mutum mu je bakin titi, amma babu motar da za ta shiga yankin. Tun lokacin gwamnatin PDP muke koke kan wannan matsala, har ga wannan gwamnati amma shiru. Mun je Karamar Hukumar Katsina mun yi koke har mun gaji. Kuma matakala kawai za a dora a saman kwalbatin da ke nan gab da kwalta a bakin Kofar Durbi, ana yin hakan an raba mu da wannan matsalar,” inji daya daga cikinsu.

Al’ummar Bakiyawa da ke Karamar Hukumar Batagarawa ma irin matsalar da suke fuskanta ke nan ta matsalar hanyar. Kamar yadda Malam Lawal Chake Mai Tireda ya ce, “Muna da kasuwa, amma babu hanya mai kyau ballantana ta hade wadannan garuruwa ta kai ga Karamar Hukumar Kurfi. Babbar matsalar ma sai lokacin damina. Mutum yana ji yana gani zai zauna gida babu wurin zuwa. Maganar zuwa da mara lafiya asibiti, sai dai ’yan dabaru, amma ba maganar bin hanya. Mun je har Majalisar Dokokin Jihar Katsina mun kai kuka, amma har yanzu babu alamar da muka gani,” inji Malam Lawal mai magana yawun Kungiyar Rayawa da Ci Gaban Bakiyawa da kewaye.