Rashin halartar lauyan da ke tsaya wa Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati yau Litinin ya dakatar da tuhumar da kotu take yi wa tsohon Gwamnan Neja Babangida Aliyu da dan takarar Gwamnan jihar Neja a jam’iyyar PDP Alhaji Umar Nasko.
Kotun dai na tuhumar Aliyu da Nasko da kuma Kwamishinan muhallli akan laifuka takwas ciki harda almundahana da kudaden kasa.
Ana tuhumar su ne, akan kudaden da yawan su ya kai Naira biliyan 1.940 wanda gwamnatin tarayya ta baiwa gwamnatin jihar a shekarar 2014.