✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin gata ne ya janyo cunkoson Fulani a gidajen yarin Kurmi – Sarkin Hausawan Abeokuta

Mai martaba Sarkin Hausawan Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ya koka bisa yadda ake tsare da dimbin  fulani makiyaya a gidajen yarin Kurmi, wadanda da…

Mai martaba Sarkin Hausawan Abeokuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ya koka bisa yadda ake tsare da dimbin  fulani makiyaya a gidajen yarin Kurmi, wadanda da yawansu ba wani laifi suka aikata ba, illa kawai jahilci da duhun kan su ne ya kai su ga haka, “ mun shiga gidajen yari da dama a wannan yanki namu inda muka iske sama da kaso uku bisa huɗu na wadanda ake tsare da su Fulani ne, abin da ya janyo haka kuwa shi ne ba su da wadanda za su karbi belinsu, mafi yawancin su ƙananan laifuka ne da su wasun su ma ba su aikata laifin komai ba, amma a saboda rashin gata na wanda zai tsaya musu sai ka ga an bar su a gidan yari, “ inji shi.
Sarkin Hausawan na Abeokuta ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake gabatar da makala a taron karin haske da kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyetti Allah, reshen Jihar Ogun ta gabatar a karshen makon jiya a  Abeokuta. Ya kuma yi kira ga shugabannin Fulanin, wadanda suka hada da harɗo-harɗo da shugabannin kungiyar miyyetti Allah da su bayar da himma don ganin an magance wannan matsalar. Ya kuma sha  alwashin yin aiki tuƙuru da shugabanin Fulanin don ganin an yi maganin matsalar, inda ya yi kira ga shugabannin Arewa da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na lauyoyi da su shigo lamarin, domin su bayar da tasu gudunmawar.
Barista Shittu Bayero lawya ne da ke yin ruwa da tsaki a al’amuran da suka shafi Fulanin a jihohin Oyo da Kwara ya shada wa Aminiya cewa, a lokuta  da dama za ka ga Fulanin sun shafe wata da  watani suna nemam dan uwansu, wasun su ma a haka suke haƙura, domin ba su san inda za su je ba.
“Ba sa iya tunkarar ofishin ‘yan sanda su bincika sabo da tsoron kada su ma  a kama su. A haka ne za ka ga ‘yan sanda sun kama Bafullatani ba tare da sun nemo ‘yan uwansa ba, sai su tsare shi  a  miƙa shi a gaban kotu, saboda su ba Turanci ko Yarbanci suke ji ba. Da zarar an tambaye su kuna da laifi sai ka ga sun ce eh, domin ba sa fahimtar abin da ake nufi.  Don haka kirana ga Fulani makiyaya shi ne su rinka sanya ’ya’yansu a makaranta, domin su ne za su rinka kare musu hakkinsu a nan gaba ba kiwon shanu kawai za su sanya a gaba ba,” inji shi.
Shugaban kungiyar Miyyetti Allah a jihohin Kurmi Alhaji Kabir Labar ya shada wa Aminiya cewa, tuni wannan matsalar ke ci musu tuwo a kwarya, domin abin tayar da hankali ne a ce Fulani ne ke da kaso hudu bisa uku a fursunonin Kurmi. Ya ce kungiyar na yin iya kokarinta don ganin an magance matsalar.
A cewar shugaban kungiyar ta miyetti Allah, reshen Jihar Ogun, Alhaji Abdulmuminu taron wanda ya samu halarcin daukacin shugabanin Fulani daga sassa daban-daban na Kurmi da ma shugabannin kungiyoyin manoma.
An shirya taron ne don ƙara wa jama’arsu haske, tare da karfafawa mambobin kungiyar su gwiwar yin aiki tukuru. Abin da ya sanya shi rantsar da shugabannin yankin da za su taimaka masa ke nan. Ya kuma rushe tsofaffin shugabannin kungiyar na kananan hukumomin jihar, tare da  bai wa hardo-hardon kowacce karamar hukuma damar zakulo amintattun mutanen da za su ja ragamar shugabancin kungiyar a matakin kananan hukuma.