Aminiya: Ko za ka fada mana fa’idar kasancewar Cocin nan da Masallaci kusa da juna a wannan gari, a yayin da ake kokarin fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Kiristoci a jihar nan?
Da farko dai zan fara godiya ga Allah, domin zaman lafiya an ce wai ya fi zaman dan sarki. Abin da ya faru har aka gina wannan Masallaci da Coci waje daya shi ne: A kwanakin baya ne al’ummar Musulmi da ke wannan gunduma na agwa a Kudanden suka zo wajena suka bukaci cewa suna so su gina masallaci, sai na ce su tafi su nemo fili.
Bayan sun samo wuri sai suka gina masallaci. Wannan masallaci ya kai kusan shekara biyu da fara gina shi. Daga baya sai suka lura wasu na gini a kusa da su. Daga nan sai suka sake dawowa wurina suka bukaci da in bincika domin sun samu labarin wai Coci za a gina a wajen.
Bayan na bincika na kuma tabbatar da cewa Coci ake ginawa sai na kira dukkansu inda na nuna masu cewa duk abin da ya shafi addini dole in bashi muhimmanci.
Na kuma basu tabbacin cewa duk abin da zamu yi domin samun zaman lafiya za mu tabbatar da cewa an yi adalci.
Na basu hakuri da su bani mako daya domin ganawa da sauran jama’a domin samun mafita. Su da kansu suka je suka zauna suka tattauna har suka fahimci juna tare da rubuta yarjejeniya a kan zaman lafiya.
Ni dai kawai sun kirani ne kafin cikar wa’adin da na diba cewa ai Abu ya zo da sauki. Suka same ni a fada na kuma saka hannu a yarjejeniyarsu. Takardar da suka rubuta shi ne dukkansu sun yarda cewa kada wani abu da za su yi a masallacin ko Coci ya cutar da daya bangaren.
Yin hakan ya faranta mini rai domin na ji dadi a raina domin wannan fahimta da suka nuna ba a samunsa a ko ina. Kuma wannan ya kara dankon zumunci da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu.
Aminiya: Akwai wani kira da za ka yi ga mazauna sauran unguwanni da ake samun rabuwan kawuna wajen ganin sun yi koyi da abin da ya auku a Kudanden?
Zan yi kira ga duk wanda Allah Ya bai wa matsayi da su fahimci cewa matsayi Allah ke badawa. Mu da Allah Ya bai wa amanar jama’a, dole mu yi kokari mu rike amana.
Ina so in yi kira ga kasa baki daya da sauran al’umma a inda ake samun irin wannan matsala da cewa akwai bukatar shugaba ya zauna ya fahinci matsalar ba tare da nuna bambanci ba.
Kada shugaba ya nuna bambanci idan har yana son yin adalci. Domin duk addinan nan namu ne, don haka a matsayinka na shugaba dole ka rungumi kowa da kyakkyawan nufi.
Domin abin da ya faru a gundumata ya nuna akwai fahimtar juna a tsakanin Musulmi da Krista da ke zauna a nan. Kuma idan aka ci gaba da yin haka, gaskiya ba za a rika samun matsaloli ko rikici na addini ba.
Rashin fahimtar juna ne ke janyo rikicin addini ko kabilanci. Amma idan aka samu shugabannin kwarai da za su taimaka ta hanyar yin wa’azin zaman lafiya tare da nuna wa talakawa gaskiya a kan zaman lafiya da amfanin zama lafiya da juna. Hakn zai sa a samu zaman lafiya a kasa da jiha da kuma a gundumomin mu.
Aminiya: Ko an taba samun rikici a tsakanin mabiya addinan nan biyu a wannan gari na Kudanden?
Gaskiya bamu taba samun rikici ba. An sha fama da rikice-rikice a jihar nan amma Allah Ya na kare wannan unguwa ko gari na kudanden.
Kamar yadda sunan yake cewa Kudanden na nufin gari mai albarka. Muna da albarka kuma muna da zama lafiya. Bamu taba samun rikici a Kudanden ba, kuma muna zaune lafiya a tsakanin Musulmi da Kiristoci. Kai har da wadanda ba su da addini ma. Akwai mutane iri-iri daban-daban a kudanden kuma duk muna zaune lafiya.
Aminiya: Wani kira za ka yi ga al’ummarka kan zama lafiya?
Kira ta garesu shi ne su rungumi zama lafiya kamar yadda aka san mu da zama lafiya shekaru da yawa da suka wuce. Mu ci gaba da zama cikin zama lafiya da juna.
Musulmi da kirista, Alla daya ne ya halicce mu. Don haka mu ci gaba da hakuri da juna ba tare da matsawa juna ba. Yin hakan ne zai bamu zama lafiya da fahimtar juna.