✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin Da’a: Masarautar Gujba ta sauke Hakimin Gabai

Dakatarwar ta fara aiki ranar Litinin 18 ga Oktoba, 2021.

Masarautar Gujba a Jihar Yobe ta dakatar da Hakimin Gabai, Ali Main Garba, bisa zargin rashin da’a da furta kalaman da ba su dace ba da kuma rashin ladabi.

Takardar dakatarwar mai dauke da sa hannun sakataren masarautar, Mohammad Ali Yusuf, ta ce dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar Litinin 18 ga watan Oktoba, 2021.

“Majalisar Masarautar Gujba ta umurce ni da na sanar da kai cewa an dakatar da kai daga matsayin Hakimin Gabai daga yanzu har sai abin da hali ya yi.

“Dakatarwar ta biyo bayan zargin ka da ake yi da faurta wasu miyagun kalamai da kuma rashin da’a da rashin mutunta masarauta.

“Hakan ne ya sa Masarautar Gujba ta dakatar da kai daga ranar 18 ga watan na Oktoba 2021, amma ana ci gaba da gudanar da bincike a kai,” inji sanarwar.

Tuni aka tura takardar dakatarwar ga Kwamishinan Kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu na Jihar Yobe da kuma Shugaban Karamar Hukumar Gulani, domin sanar da su da kuma daukar matakan da suka dace.