✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rashin biyan albashi: Ma’aikata sun rufe kamfanin jiragen Arik

Hada-hadar kamfanin sufurin jiragen sama na Arik ta fuskanci tasgaro bayan kungiyoyin kwadago sun rufe kamfanin bisa zargin rashin biyan hakkokinsu. A ranar Litinin ne…

Hada-hadar kamfanin sufurin jiragen sama na Arik ta fuskanci tasgaro bayan kungiyoyin kwadago sun rufe kamfanin bisa zargin rashin biyan hakkokinsu.

A ranar Litinin ne ma’aikatan suka zargi kamfanin da kin biyan hakkokinsu tun daga watan Afrilu, tare da tilasta wa kusan kaso 90 cikin 100 daga cikinsu ajiye aiki.

Kungiyoyin da suka hada da NUATE da ATSSSAN sun rufe dukkannin harkokin kamfanin ciki har da sauka da tashin jirage.

Shugaban ATSSSAN na kamfanin, Innocent Atasie ya ce sun dauki matakin ne bayan da hakarsu ta gaza cimma ruwa, kuma za su zarce da yajin aiki har sai kamfanin ya biya bukatunsu.

Bukatun sun hada da biyan basussukan kudadensu na ariyas, sanya hannu a yarjejeniyar aiki, fitar da kudaden fansho, haraji da sauran abubuwan da suka zama wajibi.

Sauran su ne biyan albashin da suke bi bashi na tsawon watanni bakwai ba tare da bata lokaci ba.

Lamarin ya jefa fasinjojin masu shirin tafiya cikin halin rashin tabbas, suna masu takaicinsu yadda matakin ya shafe su ba tare da sanar da su tun da farko ba.

To sai dai manajan sadarwa na kamfanin na Arik ya ce tuni suka shirya tattaunawa da kungiyoyin ma’aikatan ranar 15 ga watan Satumba domin magance matsalolin.