✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin Albashi Mai Kyau Ke sa Likitoci Kaura daga Najeriya’

Sama da kashi 70 na wani rukuni na ’ya’yan kungiyar a asibitin Jami'ar ABU ba a biya su albashin watan Agusta ba

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya ta bukaci a inganta yanayin aiki da kula da biyan hakkokin mambobinta domin takaita yadda suke barin kasar zuwa wasu kasashe domin yin aiki.

Mataimakin shugaban kungiyar, Dakta Badmus Kabir ya ce dalilan da kan sa wasunsu barin kasar nan sun hada da matsalar tsaro da rashin wadataccen albashi da rashin kyakkyawar yanayin aiki da rashin tura su karo ilimi domin su yi gogayya da tsararrakinsu.

Ya shaida wa manema labarai a Zariya cewa a halin da ake ciki, sama da kashi 70 na ’ya’yan kungiyar da suke matakin albashi na 3 da na 4 na tsarin albashin kiwon lafiya ba a biya su albashin watan Agusta ba.

Dakta Badmus Kabir ya ce kaurar likitocin zuwa wasu kasashe babban kalubale ne bangaren lafiyar Najeriyan, duba da yadda yadda hakan ke haifar da karancinsu a manyan asibitoci.

Da yake nuna takaici bisa hakan, Dakta ya ce shekaru biyu da suka wuce kungiyar na da mambobi sama da 500 amma yanzu ba su wuce su 400 ba.

Likitocin da suka tafin a cewarsa, sun hada da wadanda suka kammala samun horon neman kwarewa da kuma wadanda suka sauya wuraren aiki zuwa wasu asibitocin.

Ya bayyana cewa a sashin da yake aiki, masu mukami irin shi su 18 ne, amma ya zuwa yanzu 5 daga cikinsu sun bar Najeriya.

Dokta Kabir ya nuna damuwa bisa karuwar kananan likitoci da ke barin asibitin a shekaru biyu da suka wuce, sabanin shekarun baya da manyan likitocin ne ke tafiya.

Hakan a cewarsa zai raunana bangaren lafiya, kuma yawan yin kauran kan janyo karin aiki ga sauran likitocin, saboda “ko wata guda ba a yi ba da kungiyar ta rasa ’ya’yanta hudu a sakamakon dinbim aiki da ya karu masu.”

Ya ce baya ga likitocin da aikin ya karu masu, su kansu marasa lafiyan suna shan wahala sakamakon hakan.

Kabir ya yi bayanin cewa mutum na farko da mara lafiya zai gani shi ne karamin likita da zai dauki bayanin rashin lafiyarsa domin kai wa ga babban likita.

Manyan likitocin na ganin marasa lafiyar ne a wasu kebabbun ranaku, amma yanzu da ake da karancin likitocin, marasa lafiya da ba na gaggawa ba ana kebe masu ranar dawowa domin ganin likita har na tsawon watanni hudu ko ma fiye.

A don haka sai ya bukaci gwamnati da duk masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen bunkasa yanayin aiki da kula da biyan su kudaden alawus domin magance matsalar yin kaura da likitocin ke yi.

Ita ma a zantawar da aka yi da ita,mai magana da yawun Asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Aisha Abdulkadir ta tabbatar hakan, sai dai ta ce ba ta da yawan adadin likitocin da suka yi kaura daga asibitin.