Wani malamin addinin Kirista ya bayyana rashin adalcin shugabanni da cewa shi ne ummul-aba’isun da ke kawo tabarbarewar tsaro da aikata ta’addanci a Najeriya.
Rabaran Isaac Gbadero na na Majami’ar First Baptist da ke Sabon Garin Zariya ne ya bayyana haka a sakonsa na bikin Kirsimeti na bana ga mabiyansa.
- Sojoji sun kashe sama da mutum 30 a Myanmar, sun kone gawarwakinsu
- Ganduje tauraro ne a siyasar Najeriya — Gwamnonin APC
A cewarsa, dukkan bala’o’in da Najeriya ke fama da su a halin yanzu rashin adalcin shugabanni ne da muka sami kanmu a ciki.
Ya gargadi al’umma da su koma ga Allah tare da neman afuwarSa bisa laifuffukan da suke aikatawa.
A ranar Asabar ne dai Kiristocin Najeriya suka bi sahun dimbin takwarorinsu a fadin duniya domin bikin ranar Kirsimetin na bana.
Ana dai bikin ne don tunawa da ranar da aka haifi Annabi Isa (A.S), wato Yesu Almasihu.