Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A. Tar ta fitar, gwamnatin ta yi Allah-wadai da irin munanan kalamam da suke yi da kan iya haifar da barazana.
- An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe
- ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda matasa ke caccakar manyan jami’an gwamnati da munanan kalaman cin zarafi da cin mutuncin tare da ƙalubalantar manufofin gwamnati ba tare da cizawa su hura ba.
A cewar sanarwar wannan halayya da waɗannan matasa ke nunawa abin tur ne kuma ba abin yarda ba ne.
Don haka gwamnatin jihar tana kira ga matasanta da su kiyaye da ɗabi’un da ba su dace da al’adunmu ba.
Sanarwar ta kuma jaddada sunan jihar a matsayin ‘Gidan Zaman Lafiya’, tare da bayyana muhimmancin kiyaye zaman lafiya da juna a tsakanin al’ummominta daban-dabam.
Yayin da take amincewa da ’yancin faɗin albarkacin baki, da gudanar da taro cikin lumana da tsarin mulki ya ba su, gwamnati ta bayyana ƙarara cewa ba za ta amince da keta doka da oda ko kuma keta kundin tsarin mulki ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙofofin gwamnati a buɗe suke a kodayaushe don bayyana koke-koke na jama’a yadda ya kamata da kuma aiki mai ma’ana,” in ji sanarwar.
“Duk mai son bayyana ra’ayinsa, to ya yi hakan amma bisa manufa ta doka, kuma ’yan ƙasa su guji yin kalamai marasa daɗi kana a guji yaɗa labaran ƙarya ko nuna ƙyama domin duk wanda ya karya doka zai fuskanci fushin hukuma.’