Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta Jihar Kano, ta ce binciken da take gudanarwa a Ma’aikatar Noma ta Jihar bai shafi Mataimakin Gwamnan Jihar Nasiru Yusuf Gawuna ba.
Shugaban Hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, cikin sanarwar da ya fitar ya ce binciken ya shafi wasu jami’ai na Ma’aikatar Noma ta jihar ne amma ba Mataimakin Gwamnan ba yadda wasu kafofin sadarwa ke yadawa.
Muhuyi ya ce “yanzu haka muna ci gaba da bincike a yayin da Hukumar ta gayyaci wasu jami’ai na Ma’aikatar Noman da suka hada da wani Babban Sakatare da Darakta kuma suna bayar da gudunmuwa a kan binciken.
“Mun karbo N7,150,000 da aka karkatar da su daga ma’aikatar wanda ya saba wa sashe na 26 cikin dokokin Hukumar.
“Saboda haka duk wani yunkuri na neman jefa Mataimakin Gwamnan da zargi yaudara ce da karya.
“Domin kawar da shakku, da amincewa kuma da goyon bayan Mataimakin Gwamnan muka fara gudanar da binciken,”inji Muhiyi.