✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha za ta iya kai wa makwabtanta hari idan ta yi nasara a kan Ukraine – NATO

NATO ta ce ya zama wajibi ta taka wa Rasha birki

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce kasar Rasha na iya sake kai hari kan kasashen da ke makwabtaka da ita muddin Shugaban Kasar, Vladimir Putin ya yi nasarar a kan Ukraine.

Shugaban kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Norway.

Ya ce, “Muddin Rasha ta yi nasara a wannan yakin, Putin zai yi amannar tashin-tashina na da riba. Sannan zai hari kasashe makwabta.”

Stoltenberg ya fadi hakan ne bisa la’akari da harin da Shugaban Rasha ya kai Ukraine.

Ya kara da cewa, “Yayin da Putin ya dauka cewa zai iya samun duk abin da yake so a duniya ta hanyar amfani da karfin soja, mu kuwa hakan hatsari ne a gare mu.”

Kazalika, Stoltenberg ya ce baya ga nuna goyon baya ga Ukraine, wani aikin da ya doru a kan NATO shi ne hana rikici tsakanin kasashen biyu yaduwa zuwa wasu sassan.

A cewar Sakataren, halin da rikicin ke ciki a yanzu ya munana. Kuma Ukraine ta kimtsa kanta don maida martani kan hari a yankin Kudancin kasar.

Daga nan, ya yi gargadi kan karuwar barazanar da Rasha ke wa Norway duba da yadda Rashar ta mamaye Ukraine.

(NAN)