✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta yi wa Ukraine ruwan makamai masu linzami

Akalla makamai masu linzami 55 Rasha ta harba.

Sojojin Rasha sun harba makamai masu linzama kan Ukraine a wani kazamin hari da aka kai kan kan ababen more rayuwa da makamashi.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Jamus da Amurka suka yi alkawarin taimaka wa Kyiv da manyan tankokin yaki.

Shugaban rundunar sojin Ukraine, Valery Zaluzhny ya ce akalla makamai masu linzami 55 Rasha ta harba a sabon harin na ranar Alhamis, amma kuma sun yi nasarar harbo 47 daga cikinsu ciki har da 20 da aka harba wa babban birnin kasar Kiev.

Yayin da Rundunar Sojin Saman kasar ta yi shelar nasarar kakkabo kuramen jiragen har sama da guda 24 da sojojin Rasha suka harba daga kudancin kasar ta Ukraine.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta bi sahun Jamus wajen sanar da samar wa Ukraine tankokin yaki kirar Abrams guda 31 domin taimaka mata tunkarar mamayar da Rasha ke yi, yayin da Jamus ta ce, nata samfurin tankokin yaki na ‘Leopard’ guda 14 za su isa Ukraine kafin karshen watan Maris.

Tuni Fadar Gwamnatin Kremlin ta ce, Rasha na kallon bai wa Ukraine wadannan tankokin yakin tamkar kasashen sun shiga cikin yakin ne kai tsaye.