✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ta musanta kai hari Ukraine bayan yarjejeniyar hatsi

Rasha musanta kai hari tashar jirgin ruwa ta Odessa a Kudancin Ukraine bayan yarjejeniyar fitar da hatsi

Rasha ta nesanta kanta da harin da Ukraine take zargin ta da kaiwa a tashar jiragen ruwa na Odessa da ke Kudancin ksar bayan sun kulla yarjejeniya.

A ranar Asabar Ukraine ta zargi Rasha da kai hari da makamai masu linzami a tashar jirgen ruwa ta Odessa, sa’o’i kadan bayan sun sanya hannu kan yarjejeniyar barin Ukraine ta fitar da hatsi kasuwannin duniya.

Jin kadan bayan zargin, hukumomin Rsha suka nesanta kansu da harin, suna masu cewa kasarsu ba ta da alaka da hare-hare, kuma, “Muna lura da abin da ke faruwa da kuma tabbatar da cika alkawuran da aka yi.”

Rahotanni sun ce Rasha ta harba wa Ukraine makamai masu linzami guda hudu a ranar Asabar.

Biyu daga cikin makaman sun yi yi barna a tashar jiragen ruwan, a yayin da Ukraine ta kakkabo wasu guda biyu.

Hukumar kula da tashar jiragen ruwan ta tabbatar da hare-haren, amma ta ce ba su yi barna sosai ba.

A ranar Juma’a makwabtan biyu suka kulla yarjejeniyar sulhu don barin Ukrain ta fitar da hatsi zuwa kasashen duniya.

Yarjejeniyar da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka jagoranci kullawa ta dora musu alhakin tabbatar da cewa jiragen ruwa da ke shiga ko fitowa daga Ukraine ba su dauki makamai ba.

Mamayar Ukraine da Rasha ta kaddamar a Ukarine tun a watan Fabrairu, ya hana jigilar hatsi zuwa kasashen duniya.

Miliyoyin ton din kayan abinci da sojojin Rasha suka datse a Ukrain ya haifar da tashin gwauron abinci da barazanar yunwa ga biliyoyin mutane.