Kimanin sojojin Ukraine 13,000 ne suka mutu, wasu dubban kuma suka samu raunuka a yakin da kasarsu ke yi da Rasha.
Mykhailo Podolyak, hadimin Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zalensky, ya ce yawan sojojin da suka samu raunuka ya zarce wadanda suka mutu a tsawon wata tara da kasashen biyu ke yaki da juna.
- An sace fasinjoji cikin motar haya a hanyar Abuja
- ’Yae Ayatollah Khamenei ta bukaci kasashe su yanke hulda da Iran
Mykhailo Podolyak, ya bayyana cewa nan gaba idan hukumomin sojin kasar sun kammala tantance alkaluman sojojin da suka kwanta dama a yakin, Mista Zalenskyy zai sanar a hukumance.
A watan Satumba ne sojojin Ukraine suka kaddamar da sabbin hare-hare tare da kwace yankunan da sojojin Rasha suka kwace a Arewa maso Gabashi da Kudancin kasar, ciki har da birnin Kherson mai matukar muhimmanci.
A yayin da yanayin hunturu ya shigo kuma, ana can ana gwabza kazamin yaki tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine a yankin Donetsk.