✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rasha ta hana ’yan jaridar Birtaniya 29 shiga kasarta

Rasha ta zargi ’yan jaridar da kara rura wutar kyamar Rasha a tsakanin al’ummar Birtaniya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce gwamnatin kasar ta hana ’yan jaridar Birtaniya 29 masu dauko rahotannin yakin da take yi a Ukraine daga shiga kasarta.

Daga cikin ’yan jaridar da aka hana shiga Rasha, akwai ma’aikatan BBC da suka hada da Clibe Myrie da Orla Guerin da kuma Paul Adams, wadanda dukkansu suna dauko rahotanni ne daga Ukraine tun barkewar yakin.

Sai kuma Darakta Janar na BBC, Tim Dabie da editocin jaridun Times da Daily Telegraph da Guardian da Daily Mail da kuma Independent da ’yan jarida daga gidajen talabiji na Sky da Channel 4 da kuma ITB.

Rasha ta ce ta dauki matakin ne a matsayin martani ga takunkumin da Yammacin Turai suka kakaba wa kafafen watsa labaranta.

Rasha ta zargi ’yan jaridar da “kara rura wutar kyamar Rasha a tsakanin al’ummar Birtaniya.”

Baya ga ’yan jaridar, akwai mutum 20 da suke da alaka da harkar tsaro a Birtaniya da Rasha ta hana su shiga kasarta.

Babban Hafsan Sojin Ruwa Ben Key da manyan jami’an tsaro da na kamfanin tsaron sama na BAE System da Thales UK suna cikin jerin.