Wata kotu a birnin Moscow ta haramta amfani da Facebook da Instagram a Rasha, bayan da ta ayyana ayyukansu a matsayin masu tsauri.
Kamfanin dillacin labarai na Tass na kasar Rasha, ya ce alkalin kotun, Olga Solopova, ya yanke hukuncin ne bayan shigar da kara da aka yi kan kamfanin Meta, mamallakin Facebook da Instagram.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Kabilanci Ke Barazana Ga Hadin Kan Najeriya
- Najeriya ce kasa ta 114 mafi samar wa ’yan kasa jin dadi a duniya —MDD
Ofishin Babban Mai Gabatar da Kara na Rasha, ya ce ana yada abubuwan karya game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ta kafofin sadarwar.
Tun da farko an toshe Facebook da Instagram a Rasha kan abin da Fadar Kremlin ta kira yada labaran kanzon kurege.
Alkalin kotun ya ce hukuncin bai shafi kafar WhatsApp ba, mallakin kamfanin Meta.
Tun bayab mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine take ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashe da dama na Yammacin Turai, amma hakan bai sanya shugaba Putin ya saduda ba.