Rasha ta ce za ta iya kawo karshen ayyukan soji da ta ke yi a duk lokacin da ta so idan har Ukraine ta cimma wasu sharuddan da Rashar ta gindaya.
Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce tilas Ukraine ta amince cewa yankin Crimea mallakin Rasha ne, kuma Donetsk da Luhansk kasashe masu zaman kansu ne.
- ASUU: An kafa kwamitin magance yajin aikin Jami’o’i
- ‘Ko a Amurka da Ingila ana bai wa Mata kaso mai tsoka a siyasa’
Baya ga wadannan, Peskov ya kuma ce tilas Ukraine ta sauya tsarin mulkinta kuma ta yi watsi da niyyar shiga wata kungiya (a misali Nato).
Ya kara da cewa Rasha za ta kammala tsaftace Ukraine, kuma sai bayan an biya dukkan wadannan bukatun ne “ayyukan sojin” da dakarunta ke yi za su kawo karshe “nan take”.
Kakakin Fadar Kremlin din ya nanata cewa Rasha ba ta da niyyar mallake kasar Ukraine fiye da wanda ta yi a yanzu.
Rasha ta kwace yankin Crimea ne a watan Maris din 2014, kuma bayan wasu makonni ta goyi bayan ‘yan awaren da ke kokarin ballewa daga a yankunan Donetsk da Luhansk na gabashin Ukraine.
Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu
Tawagar Ukraine ta isa Belarus a wannan Litinin da zummar fara zaman tattaunawa karo na uku da takwarorinsu na Rasha game da kawo karshen yakin da kasashen biyu ke gwabzawa.
Wakilan Ukraine sun isa dandalin Belovezhskaya da ke kan iyakar Poland da Belarus a cikin jiragen sama biyu masu saukar ungulu domin fara ganawa da kasar Rasha wadda ke kai hari a cikin Ukraine.
A bangare guda, duk dai a yau Litinin ne shi ma shugaban Amurka Joe Biden ke ganawa ta kafar bidiyo da takwarorinsa na Faransa da Jamus da Birtaniya, inda suke tattaunawa kan abubuwan da ke wakana a tsakanin Rasha da Ukraine.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da manyan kasashen duniya suka kara kaimi a yunkurinsu na diflomasiya domin lalubo mafita game da wannan yaki na Ukraine.
Gwamnatin Ukraine da sauran shugabannin kasashen yammacin duniya sun yi ta yin kira ga shugaban Rasha Vladimir Putin da ya gaggauta kawo karshen mamayar da ya yi wa Ukraine tare da bai wa fararen hula damar ficewa daga kasar salum-alam
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu, sama da ‘yan gudun hijira miliyan 1 da dubu 700 ne suka tsare daga Ukrane a dalilin wannan yakin tare da neman mafaka a wasu wurare.
Wani sabon rahoto ya ce, mutane 13 sun rasa rayukansu a dazun nan sakamakon luguden wutar Rasha kan wani gidan gasa buredi a Ukraine.