✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha ga Amurka: Ki daina wasa da wuta

Kasar Rasha ta gargadi kasar Amurka da kada ta sake ta yi wasa da wuta, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ya sanar. Ministan Harkokin…

Kasar Rasha ta gargadi kasar Amurka da kada ta sake ta yi wasa da wuta, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ya sanar.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Labrob ne ya yi wannan gargadin a lokacin da yake mayar da martani ga kasar Amurka.

“Amurka ta daina wasa da wuta wanda zai iya haifar da matsalar da ka iya rusa kasar Rasha,” inji Labrob a lokacin da ake taron bita na kasashen Larabawa a birnin Moscow na kasar Rasha

A kwanakin baya ne aka samu labarin wani rikici da ya barke tsakanin sojoji inda aka kai wani hari ta sama wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin hayar kasar ta Rasha kusan 200, wanda ake zargin kasar Amurka da alhakin kai harin.

Ministan Harkokin Wajen na Rasha ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum biyar kuma suna ci gaba da bincike a kan lamarin, sannan ita kuma kasar Amurka tuni da karyata labarin inda ta ce ba ta da masaniya a kan harin.

Wannan harin dai shi ne hari mafi muni da ya auku a tsakanin kasashen guda biyu tun bayan yakin cacar baki.

Ita dai kasar Amurka tana kokarin kafa wani sansanin soji mai karfin soji 30,000 a bodar da ke karkashin yan kurdis a Arewacin Syriya, sannan ita kuma Rasha da Iran masu goya wa Assad baya ba su amince da wannan tsarin ba.

Bayan kusan shekara bakwai ana fafata yaki a kasar, Shugaba Assad ya fara samun galaba kwato da dama daga cikin sassar kasar. Amma kuma yakin na shirin daukar sabon salo domin domin mataimakansu na waje suna daukar abin da zafi.