✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasha 2018: Zambiya ta nemi a sake wasanta da Najeriya

A ranar Asabar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke Najeriya ta samu damar hayewa gasar cin kofin duniya da…

A ranar Asabar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke Najeriya ta samu damar hayewa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu bayan ta lallasa Zambiya da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo na Jihar Akwa Ibom.

Wannan nasara da kungiyar ta samu ne ya sa ta yi wa Zambiya nisa kuma ta kasance ita ce zakara a rukukun B da ya kunshi kasashen Zambiya da Aljeriya da Kamaru.

Najeriya dai ta kammala ne da maki 13 daga wasanni 5 yayin da Zambiya ke biye da maki 7 a wasanni 5 kuma ta kasance ta biyu.

Sai dai jim kadan bayan an tashi wasan ne rahotanni suka nuna Zambiya ta fara shirin kai Najeriya kara gaban Hukumar Shirya kwallon kafa ta Duniya (FIFA) don ganin an sake wasan.

A wata tattaunawa da kafar watsa labarin wasanni ta 90minutesgoal.com ta yi da wasu jami’an kwallon kafar Zambiya biyu Stephen Enuaga da kuma Kundah Pandawe, sun nuna akwai yiwuwar su kai Najeriya kara don ganin an sake wasan, musamman ganin yadda suka samu nasarar zura kwallo a raga  a yayin wasan amma alkalin wasan ya nuna an yi satar fage.

“Muna so a sake wannan wasa ne, saboda  mun zura kwallo a raga amma alkalin wasa ya yi mana magudi.  Don haka za mu bukaci a sake wasan, a matsayin adalci,” inji su.