Majalisar Dokokin kasar Sri Lanka ta zabi Firamininstan kasar, Ranil Wickremesinghe, a matsayin sabon Shugaban Kasar wacce ta sha fama da rikici.
Sabon Shugaban dai ya taba rike mukamin Firaministan kasar har sau shida.
- INEC ta ba Adeleke takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Osun
- Matasan da suka kware wajen ‘satar’ awakin mutane a Kano sun shiga hannu
Ranil dai ya sami kuri’a 134 ne inda ya doke babban abokin karawarsa, Dullas Alahapperuma wanda ya sami kuri’a 82 a zaben shugaban da ’yan majalisa 225 suka gudanar a ranar Laraba.
Shi kuwa dan takara na uku, Anura Kumara Dissanayake, ya tsira ne da kuri’a a uku kacal da ya samu daga mambobin jam’iyyarsa.
Mai shekara 73 a duniya, ana ganin nasarar ta Ranil a matsayin wata muhimmiyar farfadowa ga mutumin da ake yi wa kallon wanda ya mutu a siyasance.
Sabon shugaban dai ya zama Firaministan kasar bayan an tilasta wa Mahindra Rajapaksa sauka daga mukaminsa a watan Mayun bana, saboda abin da ’yan kasar suka bayyana da matsin tattalin arziki mafi muni da kasar ta taba shiga tun 1948.
Bayan guduwar tsohon Shugaban Kasar, Gobataya Rajapaksa, an nada Ranil a matsayin mai rikon mukamin Shugaban Kasar.
Rajapaksa dai ya bar kasar ne ala tilas sannan ya ajiye mukaminsa bayan masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan Colombo, babban birnin kasar, kafin daga bisani su mamaye gidansa,
Sai dai mutanen kasar da dama na cewa ba su ji dadin zaben nasa a matsayin sabon shugaban ba, saboda ba shi suka so ya maye gurbi ba, kasancewar yana cikin kunshin hambararriyar gwamnatin Rajapaksa.